Sanwo-Olu ya fitar da manufofin Gwamnatinsa da zarar ya karbi mulki

Sanwo-Olu ya fitar da manufofin Gwamnatinsa da zarar ya karbi mulki

Mun samu labari cewa Babajide Sanwo-Olu mai jiran-gado a jihar Legas ya fito da jeringiyar manufofin da yake da su da zarar ya zauna a kan kujerar gwamna a karshen watan nan na Mayun 2019.

Jaridar Vanguard tace Mista Babajide Sanwo-Olu ya bayyana manyan manufofi da ayyukan da zai soma yi a ofis. Gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta da wasu a Ikoyi da ke Legas.

Wannan gwamna mai shirin hawa kan karagar mulki yake cewa gwamnatinsa za ta zama mai sauraron koken jama’a tare da kuma nada duk wasu mukarraban gwamnati nan da watanni uku.

Sanwo-Olu yake cewa a nan da kwanaki 90 masu zuwa, zai zabi duk wadanda zai tafi da su a gwamnatinsa domin ya kama aiki gadan-gadan. Sanwo-Olu yace zai zabo kwararrun da su ka san aiki.

KU KARANTA: Duk Najeriya babu ‘Dan siyasar da ake suka iri na – Gwamnan Imo

Sanwo-Olu ya fitar da manufofin Gwamnatinsa da zarar ya karbi mulki

Babajide Sanwo-Olu zai gaji Akinwumi Ambode a Legas
Source: Depositphotos

Daga cikin abubuwan da Sanwo Olu zai fara tinkara shi ne kawo karshen matsalar cinkoson da ake samu a kan titunan Legas. Sanwo-Olu ya kuma ce zai yi maganin bola da ke yawo a kan hanya.

Haka zalika a cikin wadannan watanni masu zuwa, Jide Sanwo-Olu yace zai yi kokarin ganin ma’aikatan gwamnati sun samu kwarewar aiki yadda ya kamata domin a kai jihar Legas ga ci.

A karshe, zababben gwamnan na APC ya kuma bayyana shirinsa na gyara harkar lafiya da kuma sha’anin ilmi. Sanwo-Olu yace ba za a rage kudi ba, amma kowa zai iya samun ilmi ko ganin Likita.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel