Buhari zai garzaya jihar Gombe yau

Buhari zai garzaya jihar Gombe yau

Ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Gombe yau Litinin, 27 ga watan Mayu domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya yi a jihar yayinda wa'adinsa ya kusa karewa.

Ana karfafa tsaro a cikin garin Gombe saboda zuwan shugaban kasa saboda manyan ayyukan da zai kaddamar.

Daga cikin ayyukan da zai kaddamar shine babban farfajiyar taro na kasa da kasa a cikin kwaryar Gombe, Babban kofar shiga birnin Gombe, Filin ayije motoci, asibitin mata da yara da kuma hanyoyi da dama.

Sauran sune kwalejin ilimin aikin likitanci na jami'ar jihar Gombe, makarantar firamaren Hassan da sauran su.

Kwamishanan labaran jihar Gombe, Alhaji Umar Ahmed Nafada, yana kira da mutan jihar su fito kwansu da kwarkwatansu domin tarbar shugaban kasa.

A bangare guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin 2019 a safiyar yau Litinin, 27 ga watan Mayu.

An gudanar da bikin sanya hannun ne a ofishin Shugaban kasar da misalin karfe 11 na safe.

Tuni dai kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kudi, Danjuma Goje, Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Udoma Udo Udoma, babban mai ba Shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar dokoki, Ita Enang duk sun hallara a fadar shugaban kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel