Wani matashi ya ce gwanda mutum ya zauna bashi da addini da ya zama Musulmi ko Kirista a Najeriya

Wani matashi ya ce gwanda mutum ya zauna bashi da addini da ya zama Musulmi ko Kirista a Najeriya

- Wani dan Najeriya mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook ya sanya wani rubutu a shafinsa wanda ya danganci addinai biyu masu rinjaye a Najeriya

- Matashin yace gwara mutum ya zauna bashi da addini da ya zama Musulmi ko Kirista a Najeriya

A rubutun nasa da ya sanya a shafinsa na Facebook, Michael ya bayyana cewa marasa addini a Najeriya sun fi musulmai da kirista. A cewarsa, an bar Najeriya a baya ta bangarori da yawa na fannin cigaba, duk kuwa da rikon addini da al'ummar kasar suke dashi.

Wani matashi ya ce gwanda mutum ya zauna bashi da addini da ya zama Musulmi ko Kirista a Najeriya

Wani matashi ya ce gwanda mutum ya zauna bashi da addini da ya zama Musulmi ko Kirista a Najeriya
Source: Facebook

Ga dalilan da Michael din ya bayar a kasa:

"Ina ganin gwanda mutum ya zauna bashi da addini a Najeriya da ya zama Kirista ko Musulmi a Najeriya.

"Najeriya ta na daya daga cikin manyan kasashe da suke da rikon addini a duniya, sannan kuma ta na daya daga cikin kasashen da suka fi ko ina talauci a duniya. Sama da mutane miliyan 91 suna zaune cikin bakin talauci da kuncin rayuwa, kuma kullum talaucin karuwa yake yi.

"In dai kaji zance na wani abu na rashin cigaba a duniya to na Najeriya na daya daga ciki.

"Kasashen da basu dauki addini da muhimmanci ba, sun fi Najeriya cigaba sosai. A gani na sai Najeriya ta shafe sama da shekaru 1,000 kafin ta kamo kasar China da Japan a cigaba.

KU KARANTA: An cafke wani limami da yake kokarin sace wani yaro dan shekara 11

"Idan har addini ba zai sa muyi rayuwa kamar yadda sauran kasashen duniya ke yi ba, ina ganin addinin bashi da wani amfani a gare mu.

"Mai suke koyarwa al'umma idan suka tara su?

"Ban tunanin akwai wani mutumi wanda bashi da addini da yake rike da wani babban mukami na gwamnati a kasar? Ranar Juma'a da Lahadi, zaka gansu sun fita wuraren ibadarsu, amma ibadar da addinin nasu bai amfana mana da komai a kasar nan sai tashin hankali da bakin talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel