Akidar Fulani: Obasanjo yayi gaskiya, ku daina caccakarsa – Soyinka ga gwamnatin tarayya

Akidar Fulani: Obasanjo yayi gaskiya, ku daina caccakarsa – Soyinka ga gwamnatin tarayya

- Wole Soyinka, ya caccaki gwamnatin tarayya kan harin da ta kai ma tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo bayan yayi zargin cewa hare-haren Boko Haram yunkuri ne na musuluntar da yankin Afrika

- Soyinka yace gaskiya tsohon shugaban kasar ya fadi

- Ya kuma soki gwamnatin tarayya akan kin bin shawarar Obasanjo na kira ga hadin kai da yayi wajen magance rashin tsaro

Shahararren marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka, ya caccaki gwamnatin tarayya kan harin da ta kai ma tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo bisa ra’ayinsa da ya bayyana cewa ta’addancin yan Boko Haram da harin da makiyaya ke daukakawa sun zama shiri na mayar da yankin Afurka ta yamma yankin Fulani da kuma musuluntar da Afrika.

Soyinka ya gabatar da jawabi a lokacin bude bikin kada ganga na nahiyar Afrika karo na hudu a Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun, a ranar 25 ga watan Afrilu, 2019.

Akidar Fulani: Obasanjo yayi gaskiya, ku daina caccakarsa – Soyinka ga gwamnatin tarayya

Akidar Fulani: Obasanjo yayi gaskiya, ku daina caccakarsa – Soyinka ga gwamnatin tarayya
Source: UGC

An bude taron bikin mai take “Drumming for Future’ tare malaman al’adu na kasa da kasa da kuma kade kade daga kungiyoyi daga yankuna daban daban a fadin duniya a Abeokuta.

KU KARANTA KUMA: Kotun zaben Shugaban kasa ta yi watsi da karar da ke neman a dakatar da rantsar da Buhari

Obasanjo ya yi furucinsa ne a ranar Asabar a jihar Delta, yayinda gwamnatin tarayya a jawabinta wanda ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya saki, a ranar Talata, ta caccaki Obasanjo, inda tace yana yunkurin raba kan Najeriya duk da tsufar shi.

Haka zalika, Soyinka ya caccaki gwamnatin tarayya kan watsi da shawarar kira ga hadin kai wajen magance rashin tsaron da Obasanjo yayi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel