Fayemi ya lallasa El-Rufa'i a zaben shugabancin majalisar gwamnoni

Fayemi ya lallasa El-Rufa'i a zaben shugabancin majalisar gwamnoni

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, a ranar Laraba ya zama sabon shugaban majalisar gwamnonin Najeriya inda ya lallasa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i a zaben da aka gudanar a sakatariyar majalisar dake Abuja.

Fayemi zai cigaba daga inda gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya tsaya wanda ya shugabaninci majalisar zuwa yanzu.

Fayemi ya samu wannan nasara ne sakamakon rashin amincewa da gwamna Nasir El-rufai da gwamnonin jam'iyyar Peoples Demcoratic Party sukayi bisa ga ra'ayoyinsa na siyasa.

KU KARANTA: Majalisarmu ta baiwa Buhari goyon bayan da ya dace, inji Dogara

Fayemi ya lallasa El-Rufa'i a zaben shugabancin majalisar gwamnoni

Fayemi
Source: Depositphotos

Kungiyar gwamnonin ta samar da shuwagabanni shida a cikin shekaru 20 da suka gabata a demukardiyyan kasar.

Shugabannin sun hada da: Alh. Abdullahi Adamu, (Nasarawa, 1999 – 2004), Arc. (Obong) Victor Attah (jihar Akwa Ibom , 2004 -2006), Chief Lucky Igbinedion (Edo, 2006 – 2007), Dr. Abubakar Bukola Saraki (Kwara, 2007- 2011), Rotimi Amaechi (Rivers, 2011 -2015) da kuma Abdulaziz Yari (2015-2019).

A labari mai kama da hakan, kungiyar gwamnonin Najeriya ta kai kuka fadar shugaban kasa kan sabuwar ka'idar dokar aka samar na hana gwamnoni taba kudaden kananan hukumomin da ke karkashinsu.

Gwamnonin sun bayyana cewa hukumar NFIU ba tada ikon hanasu taba kudaden bisa ga dokar kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel