Shugaba Buhari ya jagorancin taron FEC na karshe da ministoci 31 (Hotuna)

Shugaba Buhari ya jagorancin taron FEC na karshe da ministoci 31 (Hotuna)

Dawowarsa daga kasar Saudiyya ke da wuya, Shugaba ya jagoranci taron majalisar zantarwa na karshe a wa'adinsa na farko matsayin shugaban kasan Najeriya a ranar Laraba, 21 ga watan Mayu, 2019.

Shugaban kasan ya yi amfani da wannan dama wajen mika sakon ta'aziyya ga marigayi tsohon karamin ministan kwadago, James Ocholi, wanda ya mutu sanadiyar hadarin mota a hanyar Abuja zuwa Kaduna a shekarar 2016.

Buhari ya yabawa mambobin majalisar zantarwan da sukayi murabus sakamakon wasu dalilai na cigaba.

Shugaba Buhari ya jagorancin taron FEC na karshe da ministoci 31 (Hotuna)
Shugaba Buhari ya jagorancin taron FEC na karshe da ministoci 31
Asali: Facebook

KU KARANTA: Shehu Sani yayi magana mai zafi akan harin da ya kashe mutum 30 a Katsina

Daga cikinsu akwai Kayode Fayemi wanda yayi murabus daga kujeran ministan ma'adinai domin takarar gwamnan jihar Ekiti. Sannan Kemi Adeosun wacce ta yi murabus bisa ga bita da kullin da akayi mata da zargin cewa takardar bautar kasan ajbu ta gabatar.

Kana akwai Amina Mohammed wacce tayi murabus daga kujeran ministar yanayi domin hawa kujerar mataimakiyar shugabar majalisar dinkin duniya; sannan karamin ministan yanayi, Ibrahim Jibril wanda yayi murabus domin zama sarkin Nasarawa.

Shugaba Buhari ya jagorancin taron FEC na karshe da ministoci 31 (Hotuna)
Shugaba Buhari ya jagorancin taron FEC na karshe da ministoci 31 (Hotuna)
Asali: Facebook

Daga karshe, Hajiya Jummai Alhassan tayi murabus domin takarar kujerar gwamnan jihar Taraba da Khadija Bukar Abba Ibrahim da ta koma takarar kujerar yar majalisar wakilan tarayya.

Buhari ya umurcesu su cigaba da zama a ofishinsu har ranar Talata, 28 ga wtaan Mayu, 2019 da za'a sake rantsar da shi matsayin shugaban kasa wa'adi na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel