CNM ta zargi tsohon Shugaban kasa Obasanjo da kokarin tada fitina

CNM ta zargi tsohon Shugaban kasa Obasanjo da kokarin tada fitina

Mun samu labari cewa wata kungiya mai suna The Coalition for Nigeria Movement (CNM) ta zargi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da yunkurin tada fitina da kawo hatsaniya a Najeriya.

Kungiyar ta caccaki Olusegun Obasanjo ne bayan ya zargi ‘Yan ta’addan Boko Haram da ‘Yan bindigan da ke labewa da sunan Makiyaya su na ta’adi da yunkurin maida Najeriya da yankin Yammacin Afrika Daula ta kasar Musulunci.

CNM tace wannan magana da Obasanjo yake yi, kokari ne na kawo hayaniya a kasar. Kungiyar tace kalaman tsohon shugaban kasar na iya kawo zaman dar-dar tsakanin Musulmai da kuma Kiristocin da ke zaune a cikin kasar.

Shugaban wannan kungiya mai zaman kan-ta watau Sabo Odeh yake cewa akwai lauje cikin nadi maganganun da Obasajo yake yi, inda ya kuma zargi tsohon shugaban kasar da cewa bai yi wani abin kirki a lokacin da yake ofis ba.

KU KARANTA: Bidiyon dawowar Shugaba Buhari Najeriya daga Umrah

CNM ta zargi tsohon Shugaban kasa Obasanjo da kokarin tada fitina

Ana zargin Obasanjo da yin kalamai masu iya jawo rigima
Source: Facebook

Mista Sabo Odeh yake cewa:

“Bai kamata jama’a su bari Obasanjo ya yaudare su da zakin baki ba domin babu abin da yake buri kamar ganin an gaza samun zaman lafiya a Najeriya.”

Kungiyar ta kara da cewa:

“Ba mu manta da yadda Obasanjo ya rika aika wasu wasiku a daidai lokacin da ake shirin zabe domin kawo hargitsi a kasar.”

Kungiyar tace Obasanjo ba zai iya cigaba da yaudarar mutanen kasar ba domin kowa ya gane lagonsa. Mista Sabo Odeh yace Obasanjo ne ya fara jefa kasar nan cikin rikici a lokacin da ya kyale aka dabbakar da shari’ar Musulunci.

Wannan kungiya tace:

“Ya kamata gwamnatin tarayya tayi kokarin maganin irin wadannan munanan kalamai da Obasanjo ya furta Obasanjo. Kuma zai yi wahala rikici bai kaure a sakamakon maganganun na Obasanjo ba”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel