'Yan sanda sun tsare wata shu'umar ungulu bayan jama'a sun kai rahoton ta a Aadamwa

'Yan sanda sun tsare wata shu'umar ungulu bayan jama'a sun kai rahoton ta a Aadamwa

- Rahotanni sun bayyana cewar rundunar 'yan sanda ta tsare wata shu'umar ungulu bayan jama'a sun kai rahoton ta

- Jama'a ne suka hada kai tare da kai korafin wata ungulu mallakar wata mata dake zaune a unguwar su wurin ofishin 'yan sanda

- Jama'ar sun yi korafin cewar a lokaci na karshe da suka ga wasu ungulu uku a garin su, mayakan Boko Haram sun kawo musu hari

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Adamawa, Adamu Audu Madaki, ya tabbatar da cewar rundunar 'yan sanda ta tsare wata ungulu da jama'a ke zargi a jihar. Kwamishinan ya bayyana cewar an tsare ungulun ne biyo bayan korafin da jama'a suka shigar.

Madaki ya ce a ranar Litinin ne wasu jama'a daga yankin karamar hukumar Maiha suka shigar da korafi a ofishin 'yan sanda a kan wata ungulu mallakar wata mata dake yankin su. Mazauna yankin sun ce ganin Ungulun na tayar musu da hankali, a saboda haka basu yarda da ita ba.

'Yan sanda sun tsare wata shu'umar ungulu bayan jama'a sun kai rahoton ta a Aadamwa
Ungulu
Asali: UGC

Sun yi zargin cewa a lokaci na karshe da suka ga wasu Ungulu uku a yankin su, harin mayakan kungiyar Boko Haram ne ya biyo baya.

DUBA WANNAN: An mayar da gidan yari makarantar firamare a Maiduguri

A cewar jaridar Sun, al'ummar yankin sun bukaci 'yan sanda su tilasta wa matar da Ungulun ta barin yankin da suke.

Bayan gudanar da bincike, rundunar 'yan sanda ta kama matar da Ungulun ta kuma yanzu haka an mayar da su hedikwatar 'yan sanda dake Yola domin zurfafa bincike.

Rahotanni sun bayyana cewar ana ciyar da Ungulun da naman N5,000 kullum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel