Yanzu-yanzu: Jirgi kirar Boeing 747 jibge da makamai ya dira Najeriya

Yanzu-yanzu: Jirgi kirar Boeing 747 jibge da makamai ya dira Najeriya

Sakamakon yakin Boko Haram da yaki ci yaki cinyewa a yankin arewa maso gabas, da rikicin masu garkuwa da mutane da suka addabin jihohin Arewa maso yammacin kasar musamman jihar Zamfara, Katsina da Kaduna, hukumar sojin Najeriya ta yiwo siyayya.

Rahoto daga tashar TVC na nuna cewa wani babban jirgi kirar Boeing 747-400 ya dira babban filin jirgin saman kasa da kasa ta Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja a yau Litinin, 20 ga wtaan Mayu, 2019.

Rahoton ya nuna cewa jirgin an dauke da makamai manya da kana wanda hukumar sojin Najeriya ta saya daga kasar Slovakia.

Yanzu-yanzu: Jirgi kirar Boeing 747 jibge da makamai ya dira Najeriya

Yanzu-yanzu: Jirgi kirar Boeing 747 jibge da makamai ya dira Najeriya
Source: Facebook

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai hari cocin Kaduna, sun yi garkuwa da Fasto da yan mata 10

Majiya ta nuna cewa an sayo wadannan makaman ne domin rundunar Operation lafiya dole dake yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma rundunar Operation harbin kunama dake yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

A labari mai kama da wannan, a watan Mayun 2018, Hukumar sojin Najeriya ta karbi sabbin kayayakin yaki wanda akayi oda daga kasashen waje wanda za'ayi amfani da su wajen cigaba da yaki da 'yan ta'addan Boko Haram da sauran masu aikata miyagun ayyuka a sauran sassan kasar.

Ciyaman na kwamitin karbar makamai na hukumar sojin, Olufemi Akinjobi ne ya karbi makaman a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke babban birnin tarayya Abuja. Makaman da aka sayo sun hada da alburusai, bindigogi, gurneti, nakiya, bama-bamai wasu makamai masu nisan zango.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel