Majalisa: PDP za ta tsayar da dan takara idan Goje ya janye

Majalisa: PDP za ta tsayar da dan takara idan Goje ya janye

Akwai alamu dake nuna cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zata tsayar da dan takara a shugabancin majalisar dattawa, idan har sanata Danjuma Goje (APC Gombe ta tsakiya) ya janye daga yin takara.

Majiyoyi na kusa da majalisar dattawa sun bayyana ma New Telegraph a karshen makon da ya gabata cewa jam’iyyar PDP na sanya ido akan yanayin al’amura, don ganin abunda zai faru a jam’iyyar APC, dangane da wadanda zasu tsaya takara a jam’iyya mai ci kafin ta yanke shawara akan ko ta tsaya takara.

A cewar daya daga cikin majiyan, tunda Goje ya ki bayyana ra’ayin shi na neman shugabancin majalisar dattawa ga al’umma, jam’iyyar adawa na jiran lokaci mafi dacewa don yanke shawara akan lamarin.

Majalisa: PDP za ta tsayar da dan takara idan Goje ya janye

Majalisa: PDP za ta tsayar da dan takara idan Goje ya janye
Source: UGC

A baya kuna iya tuna cewa jam’iyyar PDP ta lashe kujeru 43 daga cikin kujeru 109 na majalisan dattawa yayin da APC ta lashe kujeru 64, YPP ta samu kujera daya, yayin da yankin Arewacin Imo ta gaza lashe kujera kamar yanda lamarin a halin yanzu yake a kotu.

Majiya sun bayyana cewa PDP na cikin matukar farin ciki da Goje saboda ya kasance mai tare da ra’ayin kansa fiye da Lawan.

KU KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa, hotuna

An tattaro, kamar yanda Lawan yake neman alfarmar goyon baya daga sanatocin PDP, jiga jigan PDP har ila yau suna aiki don neman goyon baya daga sanatocin APC, wadanda zasu tabbatar ma dan takaransu nasara a lokacin rantsarwa.

Haka zalika an gano cewa PDP na iya samun nasara wajen lashe shugabancin majalisar dattawa, idan Sanata Ali Ndume (APC, Borno ta kudu) ya ki janye ma Lawan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel