Jihar Zamfara: Yan bindiga sun hallaka mutane 17 kuma suka hana jana'izarsu

Jihar Zamfara: Yan bindiga sun hallaka mutane 17 kuma suka hana jana'izarsu

Wasu yan bindiga sun hallaka akalla mutane 17 a mumunan harin da suka kai kauyukan Zamfara uku dake karamar hukumar Birnin Magaji dake jihar Zamfara, Daily Trust ta samu rahoto.

Mazaunan sun bayyana cewa yan bindiga sun shigo garin kan babura ne ranar Asabar inda suka kai hari kauyan Gidan Kaso kuma suka kashe akalla mutane 7, sannan kuma suka hana gudanar da jana'izar matattun.

Wani mazaunin garin, Tukur Yusuf, ya laburta cewa: "Sun hana jama'a gudanar da Sallar Jana'izar matattun har sai lokacin da jami'an tsaro da yan banga suka kawo agaji kauyen."

Gabanin yanzu mazauna Gidan Kaso sun gudu daga muhallansu sakamakon hare-haren yan bindiga amma suka dawo kwanan nan.

KU KARANTA: Dangote ya hau mataki na 11 cikin jerin manyan jagorori hamsin masu tasiri a duniya

Hakazalika, yan bindigan sun kai farmaki kauyen Dambo ranar Lahadi inda suka hallaka mutane 4 kuma suka kwashe musu awaki.

Wani mai idon shaida yace: "Mutane bakwai daga kauyen Kokeya da suka kawo agaji kauyen Dambo sun gamu da ajalinsu a hannun yan bindigan. An kashesu yayinda suka kokarin taimakawa wadanda harin ya shafa a garin Dan Dambo.

An nemi jawabi daga bakin kakakin hukumar yan sandan jihar amma ba'a samu isa gareshi ba yayin wannan rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel