An kama malamin makaranta ya yiwa dalibai hudu 'yan kasa da shekaru 12

An kama malamin makaranta ya yiwa dalibai hudu 'yan kasa da shekaru 12

- Dubun wani malamin makaranta ta cika, bayan an kama shi da laifin yiwa daliban shi 'yan kasa da shekaru 12 fyade

- Malamin ya amsa laifinsa, inda ya kotu ta dage sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Yuni

A ranar Juma'ar nan ne wata kotun Majistire da ke Euta jihar Legas ta kama wani malamin makaranta, mai suna Benjamin Ogba da laifin yiwa yara guda hudu, 'yan kasa da shekaru 12 fyade.

Ogba, wanda ya ke da shekaru 44 a duniya, kotu na tuhumar sa da laifi kala biyu. Sai dai ya amsa laifin nasa, kuma kotu ta hana bada belin shi.

An kama malamin makaranta ya yiwa dalibai hudu 'yan kasa da shekaru 12
An kama malamin makaranta ya yiwa dalibai hudu 'yan kasa da shekaru 12
Asali: UGC

Alkalin kotun, mai shari'a A.O Komolafe, ta tura Ogba gidan yarn da ke unguwar Ikoyi.

Da farko dai mai gabatar da kara, Insp. Emmanuel Silas ya shaidawa kotu cewa mai laifin ya aikata laifin tsakanin watan Afrilu da watan Mayu a makarantar kudi ta Shalom, dake kan hanyar Oke-Ira, kusa da titin jirgi dake unguwar Ebuta.

KU KARANTA: Tsananin duka da barazanar kisa yasa wani dattijo neman kotu ta raba auren dake tsakaninsa da matarsa

Silas ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya yiwa dalibai guda hudu masu shekaru 7 guda biyu, da mai shekaru 8 da kuma mai shekaru 12 fyade.

Kotun ta bayyana cewa laifin nashi ya sabawa sashe na 137 da kuma sashe na 172 na dokar kasa.

A karshe alkalin kotun ta daga sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel