Kano: Wani mutumi ya yiwa wata budurwa yankan rago saboda ta ki bashi hadin kai

Kano: Wani mutumi ya yiwa wata budurwa yankan rago saboda ta ki bashi hadin kai

- Dubun wani mutumi ta cika bayan an kama shi da laifin yiwa wata budurwa yankan rago, saboda ta ki bashi hadin kai ya kwanta da ita

- Lamarin ya faru a jihar Kano, yanzu haka budurwar ta n asibiti ta na karbar magani, yayin da shi kuma mutumin yake hannun hukuma

A ranar Litinin dinnan da ta gabatane wani mutumi da ba a bayyana sunansa ba daga unguwar Mandawari da ke jihar Kano, ya yiwa wata budurwa 'yar shekara 19 yankan rago a yayin da yake kokarin yi mata fyade ta ki bashi hadin kai.

LEGIT.NG ta samu rahoton cewa mutumin ya yanka budurwar ne bayan ta ki yarda ya sadu da ita.

Har ila yau, mun samu rahoton cewa mutumin ya yanka wani mutumi da ya yi kokarin ceton yarinyar daga wurin wanda ake zargin.

Kano: Wani mutumi ya yiwa wata budurwa yankan rago saboda ta ki bashi hadin kai
Kano: Wani mutumi ya yiwa wata budurwa yankan rago saboda ta ki bashi hadin kai
Asali: Facebook

A daidai lokacin da muke ba da wannan rahoton yarinyar ta na asibiti ta na karbar magani, a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Hakazalika, wanda ake zargin shi ma yana hannun hukumar 'yan sanda don gabatar da bincike akan shi kafin a yanke masa hukuncin da ya dace dashi.

KU KARANTA: Sau uku kawai na yiwa yarinyar makwabcina fyade - Wani mutumi

Mun kawo rahoton yadda dubun wani mutumi ta cika a jihar Katsina, yayin da kotu ta tura shi gidan yari bayan ta kama shi da laifin yiwa 'yar gidan makwabcinsa mai shekaru bakwai fyade har sau uku .

Ana ta samun laifuka akan fyade dai a jihohin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel