Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta soke fifikon da ke tsakanin HND da digiri a hukumomi 4

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta soke fifikon da ke tsakanin HND da digiri a hukumomi 4

Wani abun farin ciki ya samu a wasu a hukumomin gwamnati a ranar Talata, 14 ga watan Mayu, yayinda gwamnatin tarayya ta soke fifikon da ke tsakanin HND da digiri na jami’a.

Wannan sabon sauyi zai shafi dukkanin hukumomin da ke karkashin ma’aikatar cikin gida.

Hukumomin da abun ya shafa sune Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), Nigeria Immigration Service (NIS), Nigeria Prisons Service (NPS) da kuma Federal Fire Service (FFS).

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kafin yanzu, ana daukar jami’ai masu digiri da masu HND a matsayi daban-daban.

Yanzu Yanzu: Gwamnatin taraya ta soke fifikon da ke tsakanin HND da digiri a hukumomi 4
Yanzu Yanzu: Gwamnatin taraya ta soke fifikon da ke tsakanin HND da digiri a hukumomi 4
Asali: Depositphotos

Amma a sabon tsarin da aka shimfida za a dauke su ne a matsayi gguda wao matsayin Supritanda.

KU KARANTA KUMA: Wata kungiya ta maka hukumar yan sanda da EFCC a kotu, tace lallai sai an binciki Ganduje

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnatin jihar Kano ta soke banbancin da ke tsakanin HND da digiri a jihar. Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayyana hakan a bikin ranar ma’aikata wanda aka gudanar a babban filin wasa na Sani Abacha a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu a Kano.

Ganduje yayi bayanin cewa an kammala duk wani shirye-shirye don fara biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000 wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel