Mu ne ke da alhakin kashe sojojin Najeriya 11 - ISIS
Mafi munin kungiyar ta'adda a doron kasa wato kungiyar ISIS (Islamic States of Iraq and Syria),ta yi ikirarin cewa ita ce ke da alhakin kai hari kan sojojin Najeriya a makon da ya gabata wanda ya yi sanadiyar salwantar rayukan dakaru 11 kamar yadda jaridar Reuters ta wallafa.
Kamar yadda ta wassafa a kafar watsa labaran ta ta AMAQ, kungiyar ISIS ta yi ikirarin cewa mayakan ta ke da alhakin kai mummunan hari a garin Gajiganni da ke jihar Borno a ranar Juma'ar da ta gabata.
Kafar sadarwa ta AMAQ a ranar Asabar ta watsa wasu hotuna dake haskaka irin munin ta'addanci da kungiyar ISIS ta yiwa dakarun sojin Najeriya a sansanin su wajen bayyana konannun gawawwakin su da kuma muhallai.
Majiyoyin rahoto da dama sun bayyana cewa, mayakan ISIS haye akan babura sun zartar da wannan mummunan hari ta hanyar harbin harsashin bindiga kan mai uwa da wabi da ya auku da misalin karfe 6.30 na Yammacin ranar Juma'a ta makon da ya gabata.
KARANTA KUMA: Boko Haram: Har yanzu akwai babban yanki a jihar Borno da ba a iya shiga - Osinbajo
Kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram wadda ta zame jikin ta daga kungiyar ISIS a shekarar 2016, ta ci gaba da razanar da al'ummar Najeriya wajen zartar da ta'addanci cikin tsawon shekaru goma da kawowa yanzu rayukan kimanin mutane 30,000 sun salwanta.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng