Jama’ar Sabon Birni sun tsere sun bar gidajen su bayan harin yan bindiga

Jama’ar Sabon Birni sun tsere sun bar gidajen su bayan harin yan bindiga

Jama’ar kauyuka da dama a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto sun tsere daga gidajensu domin tsiratar da rayuwarsu yayinda yan bindiga suka kai hari kauyukansu.

Gidan talbijin din TVC ta ruwaito cewa mazauna kauyuka da dama sun koma Gatawa domin neman mafaka yayinda sauran mutane suka tsere zuwa kauyukan jumhuriyar Nijar.

Wata majiya, ta ruwaito cewa an tura jami’an soji yankin sannan kuma an kashe yan bindiga da dama yayinda wasu da dama suka raunana a musayar wuta da akayi tsakanin yan bindigan da sojoji.

Har ila yau, a wani lamari makamancin haka, an rahoto cewa yan bindiga sun kai hari kauyen Wangini da ke karamar hukumar Batsari na jihar Katsina, inda suka kashe mutum guda tare da raunata wasu uku.

KU KARANTA KUMA: Tarin motocin alfarma: Me zaka fada ma Allah – Gudaji Kazaure ya tambayi Dino Melaye

A cewar jaridar Daily Trust, yan bindigan sun kai farmaki kauyen da tsakar dare, inda suke ta harbi ba kakkautawa. Sun cinnawa motoci da gidaje mallakat mazauna garin wuta.

Legit.ng ta rahoto cewa akwai alamun cewa yawan faashi da makami da sace-sacen mutanea yankin arewa maso yammacin Najeriya na iya kawo matsalar abinci a yankin da kusan kaso 50 cikin dari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel