Mai kamfanin BUA, Rabiu, yana sake kutsawa cikin Attajiran Duniya

Mai kamfanin BUA, Rabiu, yana sake kutsawa cikin Attajiran Duniya

Mun ji cewa babban Attajirin nan na Arewacin Najeriya Abdulsamad Rabiu, wanda yayi fice wajen harkar siminti da kuma sukari yana cigaba da samun karin dukiya a halin yanzu bayan ya saye wani kamfanin siminti a Najeriya.

Alhaji Abdulsamad Rabiu ya saye kamfanin simintin nan na Kalambaina, kamar yadda kamfanin CCNN su ka bayyana kwanaki. Wannan yarjejeniya ne da aka yi ne ya sa dukiyar sa ta karu da Dala miliyan 650 a cikin shekarar nan.

A 2016, Abdulsamad Rabiu ya zo cikin masu kudin Najeriya da Afrika inda aka sa shi a matsayin mutum na 1577 da ya fi kowa kudi a Duniya. A lokacin Rabiu ya ba sama da Dala biliyan 1.1 baya, kuma shi ne ya zo na 23 a kaf fadin Afrika.

KU KARANTA: Wanda aka sacewa 'ya 'ya yace ba zai biya kudin fansa ba

Mai kamfanin BUA, Rabiu, yana sake kutsawa cikin Attajiran Duniya

‘Dan Gidan Isiyaka Rabiu ya zama Mai kudi na 23 a Nahiyar Afrika
Source: Twitter

A wannan shekara ta 2019, The billionaires' club, ta rahoto cewa Alhaji Rabiu ya mallaki fiye da Dala biliyan 1.9 a akawun din sa. Asali Rabiu ya shiga kasuwanci ne bayan Mahaifin sa, Alhaji Isiyaka Rabi’u ya ba sa wani makeken fili.

Abdussamad Rabiu shi ne shugaban kamfanin BUA da aka kafa a karshen 1980s. A shekarar 2005 ne Samad Rabiu ya bude kamfanoni 2 masu aikin fulawa a Legas da kuma Garinsa Kano. Daga baya kuma ya shiga harkar mai a 2008.

Daga cikin sauran hanyoyin da Alhaji Abdussamad Rabiu ya samu dukiyarsa akwai tashashohin jiragen ruwa da ya bude a Kudancin Najeriya da kuma manyan kamfanonin siminti da kamfanin jan wuta da harkar filaye da sauran su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel