Tashin hankali: wata guguwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, ta lalata gidaje 200 a jihar Bauchi

Tashin hankali: wata guguwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, ta lalata gidaje 200 a jihar Bauchi

- Wata bakar guguwa mai karfin gaske ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku jihar Bauchi

- Bayan haka guguwar ta yi sanadiyyar lalacewar gidaje sama da dari biyu a yankin da abin ya shafa a jihar

Mutane uku sun mutu, sannan sama da gidaje 200 sun lalace sanadiyyar wata mahaukaciyar guguwa da ta taso a garin Misau da ke jihar Bauchi.

Wani jami'in yada labarai na karamar hukumar Misau, Mista Usman Yerima, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin lokacin da suka yi hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a wayar tarho.

Yerima ya bayyana cewa mutanen ukun da suka ransu, biyu maza ne da kuma wata karamar yarinyar, yayin da gidaje sama da dari biyu suka lalace sanadiyyar mahaukaciyar guguwar.

Tashin hankali: wata guguwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, ta lalata gidaje 200 a jihar Bauchi

Tashin hankali: wata guguwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, ta lalata gidaje 200 a jihar Bauchi
Source: Facebook

Ya ce yawancin gidajen da abin ya shafa, iskar ta dauke rufin su lokacin da ta taso, sannan ya kara da cewa iskar ta yi kimanin awa 4 ba ta tsaya ba.

Da aka tuntubi diraktan hukumar taimakon gaggawa na jihar, Alhaji Kabiru Yusuf Kobi, ya ce har yanzu bai samu wani rahoto ba daga manyan garin.

KU KARANTA: Da duminsa: An sanya dokar hana fita a jihar Bauchi

"Mun ji kuma mun gani a kafafen sada zumunta na zamani, amma har yanzu gwamnati ba ta sanar damu faruwar lamarin ba.

"Zan sanar da ku ainahin yadda lamarin ya faru ranar Talata, idan na dawo daga tafiyar da zanyi, saboda muna so mu samu rahoton farko," in ji Yusuf Kobi.

Hakazalika zaku je cewar an sanya dokar ta baci a wasu yankuna na jihar Bauchi, sanadiyyar wani rikici da ya barke tsakanin matasan yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel