Da duminsa: Dan marigayi Ado Bayero ya zama sabon sarkin Bichi

Da duminsa: Dan marigayi Ado Bayero ya zama sabon sarkin Bichi

Gwamnatin jihar Kana ta nada Allhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Bichi, daya daga cikin sabbin masarautun da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkira a Kano.

Gwamnatin jihar ta kuma tabbatar da daga darajar hakiman Karaye, Rano da Gaya zuwa sarakuna masu daraja ta daya.

Hakiman da aka yiwa karin girma suna sarakunan sun ne; Alhaji Tafida Abubakar II (Sarkin Rano), Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya (Sarkin Gaya) da Dakta Ibrahim Abubakar II (Sarkin Karaye).

A yayin da ya ke tabbatar da wannan nadin, Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya ce sabbin sarakunan za su karbi takardun kama aikinsu a ranar Asabar a filin wasan na Sani Abacha a Kano.

Da duminsa: Dan marigayi Ado Bayero ya zama sabon sarkin Bichi

Da duminsa: Dan marigayi Ado Bayero ya zama sabon sarkin Bichi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya

Kafin nadinsa, Aminu Bayero shine mai rike da sarautar Wamban Kano wadda sarki Muhammadu Sanusi mai ci yanzu ne ya yi masa wannan nadin bayan ya daga darajar tsohon Wambai, Alhaji Abbas Sanusi zuwa Galadima bayan rasuwar marigayi Galadiman Kano Tijjani Hashim.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa ta samu nagartatun bayyanai da ke nuna gwamna Ganduje ya yi taro da Aminu Bayero Chiroman Kano, Nasiru Bayero da wasu hakimai daga Rano, Gaya da Karaye a daren ranar Alhamis a gidan gwamnatin gwamnatin.

Wata majiyar ta bayyana cewa Nasiru Bayero, Ciroman Kano aka fara yiwa tayin sarautan Bichi amma nan take ya ce baya ra'ayi.

Hakan yasa gwamnan ya yiwa yayan Chiroma, Aminu Bayero tayin inda ya ce yana bukatar ya yi shawara.

Zabin Ganduje na uku shine Galadiman Kano, Abbas Sanusi, mahaifin shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas sai dai shima ya ce baya ra'ayin zama sarkin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

KU LATSA: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel