Innalillahi wa inna illaihi raji’un: Magaji Ubandoman Gombe ya rasu yana da shekara 80 a duniya

Innalillahi wa inna illaihi raji’un: Magaji Ubandoman Gombe ya rasu yana da shekara 80 a duniya

Wani babban jigon kasar kuma tsohon minister a jumhuriya ta biyu, Alhaji Magaji Mu’azu (Ubandoman Gombe) ya rasu a yammacin ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu yana da shekaru 80 a duniya.

Ya rasu bayan yayi fama da jinya a babbar asibitin koyarwa ta tarayya da ke Gombe inda ya kwashe wasu watanni yana samun kulawar likitoci.

A cewar majiyoyi na iyalansa, za a yi sallar jana’izarsa a yau Litinin, 6 ga watan Mayu da misalin karfe 4:00 na rana a fadar sarkin Gombe.

An haifi marigayin a ranar 14 ga watan Maris, 1939 a Gombe, ya kuma rike manyan mukamaki a kasar.

Innalillahi wa inna illaihi raji’un: Magaji Ubandoman Gombe ya rasu yana da shekara 80 a duniya

Innalillahi wa inna illaihi raji’un: Magaji Ubandoman Gombe ya rasu yana da shekara 80 a duniya
Source: UGC

A shekarar 1977, ya gaji mahaifinsa, marigayi Mu’azu Halilu a matsayin Ubandoman Gombe kuma babban jigo a masarautar Gombe.

KU KARANTA KUMA: Ramadan: Saraki ya bukaci Musulmai da su roki zaman lafiya da tsaro

Marigayin ya kuma kasance Shugaban jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN) daga shekarar 1979 zuwa 1980 a lokacin jumhuriya ta biyu. A 1980, aka nada sa a matsayin a matsayin babban hadimin Shehu Usman Aliyu Shagari a jihar Gongola.

A 1983 lokacin da shugaba Shagari ya sake lashe zabe, sai aka nada Mu’azu a matsayin ministan tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel