Ba zan take yancin kowa ba idan na zama shugaban majalisar dattawa – Ndume

Ba zan take yancin kowa ba idan na zama shugaban majalisar dattawa – Ndume

- Sanata Mohammed Ali Ndume ya ki janye kudirinsa na son zama Shugaban majalisar dattawa na gaba

- Sanata mai wakiltan yankin Borno ta kudu a majalisar dokokin kasar, yace ba zai yi jayayya da yancin majalisar dattawa ba idan aka zabe shi a matsayin Shugaban majalisar

- Ndume yace ya cancanci taka wannan rawar ganin, inda ya kara da cewa tarihin da ya kafa a majalisar dokokin kasar na iya tabbatar da hakan

Sanata mai wakiltan yankin Borno ta kudu a majalisar dokokin kasar, Mohammed Ali Ndume, ya bayyana cewa ba zai yi jayayya da yancin majalisar dattawa ba idan aka zabe shi a matsayin Shugaban majalisar a yayin rantsar da majalisa na tara.

Ndume yace yana son jagorantar majalisar dattawa ta tara ne, domin ya taimaka waje ganin majalisar dokokin kasar tayi shugabanci naari, inda ya kara da cewa majalisar na bukatar tsayayyen mutum daga yankin arewa maso gabas da zai jagorance ta.

Ya fadi hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu.

Shugabancin majalisa: Ba zan yi jayayya da yancin yan majalisa ba – Ndume

Shugabancin majalisa: Ba zan yi jayayya da yancin yan majalisa ba – Ndume
Source: Facebook

Yace yankin arewa maso gabas ta fuskanci babban kalubale inda aka lalata dukiyoyi da ya kai sama da naira triliyan biyu sakamakon ayyukan ta’addanci, inda ya kara da cewa akwai bukatar samun tsayyayen dan takara daga yankin domin ya shugabancin majalisar dattawa, don nemo goyon bayan duniya wajen daidaita yankin.

KU KARANTA KUMA: Kwamishinan yan sandan Katsina ya koma Daura kan sace Magajin Gari

Yace ya cancanci taka wannan rawar ganin, inda ya kara da cewa tarihin da ya kafa a majalisar dokokin kasar na iya tabbatar da hakan.

Dan majalisan yace akwai haske sosai a yiwuwar zamansa Shugaban majalisar dattawa na gaba, inda ya kara da cewa yana da kyakyawar alaka da sauran takwarorinsa; masu dawowa da sabbin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel