Muhimman fa’idojin watan Ramadan guda 11 daya kamata Musulmi ya sani

Muhimman fa’idojin watan Ramadan guda 11 daya kamata Musulmi ya sani

A ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, wanda yayi daidai da 1 ga watan Ramadana ne Musulman duk duniya suka dauki azumi dake alanta shiga sabuwar wata mai albarka, watan Azumin Ramadana, watan da Allah mai girma da daukaka ya sauko da Al-Qur’ani.

Legit.ng ta ruwaito a daren Lahadi, 5 ga watan Mayu ne mai alarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da fara azumin Ramadana, inda yace sun samu labarin ganin sabon watan Ramadana a jahohin Yobe, Sokoto da Kebbi.

KU KARANTA: NYSC ta bayyana abinda yasa Boko Haram suka yi awon gaba da matashi dan bautan kasa

Da wannan ne muka kawo muku wasu muhimman fa’idoji da falalar Azumin watan Ramadan ga Musulman dake gudanar da azumin kamar yadda Allah Ya umarta a cikin littafi mai tsarki, Al-Qur’ani.

1- Azumi na kara ma Musulmi Imani

2- Azumi na sanya ma Musulmi tausayin na kasa

3- Azumi na rage ma dan Adam sha’awa

4- Azumi kariya ne ga Musulmi daga azabar wuta

5- Azumi na kankare zunubbai

6- Azumi na ceton Musulmi a ranar kiyama

7- Mai yawan Azumi zai shiga Aljannah ta kofar Rayya

8- Azumi na kara dankon zumunci a tsakanin Musulmai

9- Azumi na samar da kiwon lafiya mai inganci kama daga tsafta zuwa lafiyar jiki.

10- Azumi na samar da cikakken nutsuwa ga Musulmi yayin gudanar da ibada

11- Azumi na sanya Musulami su kasance masu juriya a lokcin kunci

Da fatan Allah madaukakin Sarki Ya kaimu zuwa ga karshen wanann Azumi, cikin lafiya da kwanciyar hankali, Aamin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel