Yanzu Yanzu: Yakubu Gowon ya yanke jiki ya fadi a wajen jana’iza a Delta

Yanzu Yanzu: Yakubu Gowon ya yanke jiki ya fadi a wajen jana’iza a Delta

- Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya yanke jiki ya fadi a lokacin jana’izan Manjo Janar David Akpodiete Ejoor

- Lamarin ya afku ne a jihar Delta yayinda ake jawabi a wajen jana'izan

- Wasu manayan sojoji sun yi gaggawan daukar tsohon Shugaban kasar zuwa wani rumfa na mussamman da aka tanada domin agajin gaggawa, sanna ya farfado faga bisani

Janar Yakubu Gowon, tsohon Shugaban kasar Najeriya ya yanke jiki ya fadi a lokacin jana’izan Manjo Janar David Akpodiete Ejoor a garin Ovwor-Olomu, karamar hukumar Ughelli ta kudu da ke jihar Delta.

Lamarin ya afku ne a gefen kabarin yayinda ake jawabi a jana’izar.

Wasu manayan sojoji sun yi gaggawan daukar tsohon Shugaban kasar zuwa wani rumfa na mussamman da aka tanada domin agajin gaggawa yayinda Gwamna Arthur Ifeanyi Okowa da Cif James Onanefe Ibori, tsohon gwamnan jihar Delta suka koma wajen don tabbatar da farfadowarsa.

Yanzu Yanzu: Yakubu Gowon ya yanke jiki ya fadi a wajen jana’iza a Delta
Yanzu Yanzu: Yakubu Gowon ya yanke jiki ya fadi a wajen jana’iza a Delta
Asali: Depositphotos

Nan take aka turo motocin daukar marasa lafiya na jihar Delta zuwa gaban rumfar esaboda koda lafiyar tsohon Shugaban zai ci gaba da tabarbarewa.

KU KARANTA KUMA: APC ta hadu da cikas yayinda kotu ta dakatar da zababben dan majalisar wakilai na Adamawa

Bayan dan wani lokaci sai aka gano Cif James Onanefe Ibori da Gwamna Arthur Ifeanyi Okowa na fitowa daga rumfar na mussaman, wanda hakan ya nuna cewa tsohon Shugaban kasar ya farfado

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel