An kashe mutane biyu a wurin biki a jihar Nasarawa

An kashe mutane biyu a wurin biki a jihar Nasarawa

- Wani rikici da ya barke tsakanin kabilar Hausawa da kabilar Yeskwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da asarar dukiya mai tarin yawa

- Rikicin wanda ya faru a daidai lokacin da ake gabatar da wani biki a karamar hukumar Karu da ke cikin jihar Nasarawa

An kashe mutane biyu a lokacin da ake gabatar da wani biki a garin Panda, da ke karamar hukumar Karu cikin jihar Nasarawa a ranar Talatar nan da ta gabata.

Mun samu rahoton cewa rikicin ya barke ne tsakanin 'yan kabilar Yeskwa da kuma Hausawa, yayin da ake zargin cewa yaran Hausawa sun jefi 'yan kabilar Yeskwa, wadanda suke biki a garin Panda.

Wata majiya ta bayyana cewa rikicin ya faru saboda kokarin da yaran suke na dakatar da bikin, sai suka dinga jifansu, har suka samu wani malamin addinin musulunci.

An kashe mutane biyu a wurin biki a jihar Nasarawa

An kashe mutane biyu a wurin biki a jihar Nasarawa
Source: Getty Images

Ya ce, "Daga binciken da na gabatar, na fahimci cewa an kai wa mai garin, Joel Oninge rahoton rikicin da ake yi, amma kafin ya hada kan shugabannin kabilun domin ya sasanta su, har wasu matasa kabilar Hausa sun zo fadar shi da bukatar dalilin da ya sa masu bikin suka jefi malaminsu.

"Sun bata abubuwa da yawa a fadar sarkin, sannan an kashe mutane biyu."

Da ya ke tabbatar da abinda ya faru ga manema labarai, shugaban karamar hukumar Karu, Samuel Akala, ya ce rikicin ya faru da safiyar ranar Talata, lokacin da wasu yara suka dinga jifan 'yan bikin.

KU KARANTA: An kama wadanda suka sace Hakimin Daura

Ya ce, "Bincike ya nuna cewa 'yan bikin sunyi kan yaran ne da niyyar tsorata su, domin su tsira da lafiyarsu, a garin haka ne har suka je suka jefi malamin.

"Abin babu dadin ji, ace an kashe mutane har biyu saboda wannan sabanin da aka samu, amma dai zuwan jami'an tsaro ya sa komai ya lafa a yanzu."

Kwamishinan 'yan sandan jihar Bola Longe, ya ce mutane biyu sun mutu sanadiyyar rikicin, ya kara da cewa yanzu haka jami'ansu na nan na bincike akan wadanda ke da hannu a kisan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel