Babar Sanata Dino Melaye ta rasu

Babar Sanata Dino Melaye ta rasu

Fitaccen Sanatan nan mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Dino Melaye ya tafka babban rashi sakamakon mutuwar mahaifiyarsa, Uwargida Comfort Melaye.

Legit.ng ta ruwaito Sanata Dino Melaye ne ya bayyana haka da kansa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa Uwargida Comfort ta rasu ne bayan ta sha fama da rashin lafiya.

KU KARANTA: Mutuwa riga: Diyar tsohon gwamnan jahar Neja ta rigamu gidan gaskiya

Babar Sanata Dino Melaye ta rasu

Babar Sanata Dino Melaye ta rasu
Source: Facebook

Tabbas mutuwa na kan kowa, idan za’a tuna a ranar Alhamis 2 ga watan Mayu ne iyalan tshon gwamnan jahar Neja, marigayi Abdulkadir Kure, suka tafka babban rashi na rasuwar guda daga cikin yayan marigayin, Malama Fatima Kure.

Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana alhininsa game da rashin Fatima ta bakin kaakakinsa, Malam Jibrin Ndace, inda ya taya iyalan Kure jimamin mutuwar yar uwarsu Fatima wanda ta rasu a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan yayi addu’ar Allah Ya jikan Fatima, kuma Ya sanyata cikin Aljannar Firdausi, sa’annan yayi addu’ar Allah Ya baiwa kafatanin danginta hakurin rashinta, Amin.

Shima mahaifin Fatima, marigayi Abdulkadir Kure wanda ya taba zama gwamnan jahar Neja daga shekarar 1999 zuwa 2007, inda daga bisani matarsa Hajiya Zainab Kure ta zama Sanata a jahar Neja, ya rasu ne a ranar 8 ga watan Janairun 2017.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel