Kasar UAE tayi sabbin dokokin hukunta mazan dake yiwa mata kallon kurilla

Kasar UAE tayi sabbin dokokin hukunta mazan dake yiwa mata kallon kurilla

- Tarayyar kasar Larabawa ta bayyana cewa zata rufe, sannan zata kuma ci taran duk wanda aka kama da laifin kallo na sha’awa wanda ke iya hana mata walwala

- Wassu daga cikinlaifuffukan sun hada da kira da baki, kallo da wata manufa daban, ajiye lambobin waya da nuna ra’ayin lalata

- A cewar dokar UAE, za’a yanke ma masu laifi hukuncin zama a gidan yari har na tsawon shekara daya ko kma taran da ba zai wuci Dh10,000 ba ko kuma dukkan hukkuncin gaba daya

Tarayyar kasar Larabawa (UAE) tayi sanarwa kan cewa duk wada aka kama d kallo da zai sa mata su kasance cikin rashin walwala kaman kira da baki, kallo mai tsanani, ajiye lambobin waya da sauran su zai fuskanci hukuncin zama a gidan yari tare da tara.

Khaleej Times ta rahoto cewa rundunar yan sandan Dubai ta karfafa gargadi yayin da ta bada sanarwa cewa a kwanakin nan ne ta kama mutane 19 bayan an kama su da laifin cin zarafin mata a bakin teku da kuma hanyoyi.

A Kasar larabawa, wannan irin cin zarafin har ila yau ya hada da kyafta musu ido, sumba da kuma yin maganganun batsa. Daukan hotunan mata ba tare da izinin su ba yana daga cikin laifuffukan.

Kasar UAE tayi sabbin dokokin hukunta mazan dake yiwa mata kallon kurilla
Kasar UAE tayi sabbin dokokin hukunta mazan dake yiwa mata kallon kurilla
Asali: UGC

Darekta na kasa na sashin binciken masu laifi, Birgadiya Jamal Salem Al Jallaf, yace mata suna da daman a basu kariya da tsaro, ya kara da cewa wadannan irin laifuffukan cin zarafin sun saba ma al’adun kasar larabawa.

KU KARANTA KUMA: Jirgin makarantar koyon tuki ya yi saukar bazata a Ilorin

Ahmad AlSayyed, babban lawya a Charles Russell Speechlys da ke London, yace wannan irin laifin- ko da yake ba babba ba ne - yana iya zuwa da hukuncin kora daga kasan.

Lamarin yafi cikawa da masu zuwa bakin teku don shakatawa.

Har ila yau, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Pope Francis ya sake gabatar da rokonsa don yafiya kan duk wani rashin adalci a mulkin da mambobin coci da cibiyoyinta ke yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel