Karuwanci: Kotun Abuja ta yankewa Mata 27 hukuncin dauri na wata guda

Karuwanci: Kotun Abuja ta yankewa Mata 27 hukuncin dauri na wata guda

A ranar Litinin din da ta gabata wata kotun tafi-da-gidan-ka da ke zaman ta a garin Abuja, ta yankewa wasu Mata 27 hukuncin dauri na wata guda a gidan dan kande a sakamakon aikata laifi na mummunar sana'a ta kasuwanci.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ababen zargin 27 da suka shiga hannun hukuma a tsakanin ranakun Laraba da kuma Alhamis, sun samu sassaucin hukunci yayin da kotun ta ba su zabin biyan tara ta Naira dubu uku a kan ko wane daya daga cikin su.

Karuwanci: Kotun Abuja ta yankewa Mata 27 hukuncin dauri na wata guda

Karuwanci: Kotun Abuja ta yankewa Mata 27 hukuncin dauri na wata guda
Source: Facebook

Alkaliya mai shari'a, Jennifer Ogbodu, yayin bayyana dalilin zartar da wannan hukunci ta bayar da shaidar cewa, kotun ta kama Matan dumu-dumu da aikata laifin da ya sabawa dokar kasa da kuma da'a a zamantakewar al'umma.

Rahotanni sun bayyana cewa, tuni Matan 27 sun yi azamar biyan tarar Naira dubu uku domin kauracewa zama gidan dan Kande biyo bayan zabi na rangwamin hukunci da kotun ta zartar a kansu.

KARANTA KUMA: Dole gwamnati ta zage dantse wajen kawar da kalubalan da ake fuskanta a Najeriya - Sultan

Mukaddashin kakakin hukumar 'yan sanda na garin Abuja, ASP Gajere Danjuma, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari yayin shaidawa manema labarai tiryan-tiryan yadda Mata 65 suka shiga kuma bincike ya tabbatar da zargi a kan 27 daga cikin su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel