Masarautar Machina ta nada gwamnan jahar Yobe wani muhimmin sarauta

Masarautar Machina ta nada gwamnan jahar Yobe wani muhimmin sarauta

Mai martaba sarkin Machina, Mai Machina Bashir Albishir Bukar ya karrama gwamnan jahar Yobe, Gwamna Ibrahim Gaidam da wata babbar sarauta a masarautarsa sakamakon gudunmuwa da cigaban daya bayar ma masarautar da jahar Yobe gaba daya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mai Machina ya karrama da Ibrahim Gaidam ne da sarautar a ranar kammala bikin al’aduna Machina da aka share kwanaki hudu ana gudanarwa a garin Machina, wanda gwamnan da kansa ya halartar.

KU KARANTA: Najeriya ta samu sabbin taragon jirgin kasa na zamani guda 10 – Minista

Masarautar Machina ta nada gwamnan jahar Yobe wani muhimmin sarauta

Masarautar Machina ta nada gwamnan jahar Yobe wani muhimmin sarauta
Source: UGC

Mai Machina, Bashir Albishir Bukar ya nada Gwamna Ibrahim Gaidam sarautar ‘Shettima Mafatihuma na Machina”, inda ya mika masa takardar nadin nasa a ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilu.

Sarkin ya bayyana ma Gwamna Gaidam cewa ya cancanci wannan sarauta ne duba da babban aikin da yayi na sake gina babbar hanyar Nguru zuwa Machina, tare da samar da tsaftataccen ruwan sha ga masarautar.

Masarautar Machina ta nada gwamnan jahar Yobe wani muhimmin sarauta

Masarautar Machina ta nada gwamnan jahar Yobe wani muhimmin sarauta
Source: UGC

Daga karshe Mai Machina ya kara da cewa ana shirya wannan bikin al’adu a duk shekara ne don karfafa al’adun Machina, tare da kara hada kan jama’an masarautar.

Shima a nasa jawabi, Gwamna Gaidam ya bayyana amincewarsa da wannan sarauta, kuma ya jinjina, tare da gode ma Sarkin Machina bisa duba cancancantarsa ta samun wannan sarauta, inda yayi fatan cigaba da bada gudunmuwa ga cigaban masarautar.

Gwamna Gaidam ya kwashe shekaru goma akan karagar mulkin jahar Yobe tun zamani marigayi Gwamna Mamman Ali wanda yayi masa mataimaki, inda bayan rasuwar Ali ya zamo gwamna, a yanzu haka ya lashe zaben Sanata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel