Rashin tsaro: Za mu kara adadin ma'aikatan hukumomin tsaro a Najeriya - Buhari

Rashin tsaro: Za mu kara adadin ma'aikatan hukumomin tsaro a Najeriya - Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, a ranar Litinin ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kudiri aniyyar kara yawan adadin ma'aikatan hukumomin tsaro domin tsananta yaki da ta'addanci a fadin kasar nan.

Rashin tsaro: Za mu kara adadin ma'aikatan hukumomin tsaro a Najeriya - Buhari

Rashin tsaro: Za mu kara adadin ma'aikatan hukumomin tsaro a Najeriya - Buhari
Source: UGC

Shugaban kasa Buhari kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito ya kuma bayyana cewa, zai nemi hadin gwiwar dukkanin jam'iyyun siyasa da ke fadin kasar cikin wa'adin gwamnatin sa na biyu domin inganta jin dadin al'ummar kasa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya bayyana hakan ne yayin halartar taron budar kai na sabbin zababbun gwamnoni da masu dawowa karo na biyu da aka gudanar cikin dakin taro na Baquet da ke fadar Villa a garin Abuja.

Shugaban kasa Buhari wanda mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilta a taron ya jaddada muhimmanci samar da tsaro a Najeriya. Ya nemi hadin gwiwar dukkanin jam'iyyun siyasa na kasar nan wajen tallafawa gwamnati domin inganta jin dadin al'umma.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda ta cafke masu tayar da zaune tsaye 264 a jihar Anambra

Kazalika shugaban kasar ya jaddada tsayuwar dakansa wajen ci gaba da tunkarar ta'addancin masu garkuwa da mutane, kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, rikicin makiyaya da manoma da kuma sauran ababe masu tayar da zaune tsaye.

Domin zage dantsen gwamnatin sa wajen cimma wannan babbar manufa, shugaban kasa Buhari ya kudiri aniyyar kara adadin ma'aikatan hukumomin tsaro a fadin kasar da za su bayar da gudunmuwa wajen dawo da martaba ta kwanciyar hankali a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel