Yan kasuwa suna ji a jikinsu bayan Sojoji sun rufe wata babbar kasuwar hatsia da dabbobi

Yan kasuwa suna ji a jikinsu bayan Sojoji sun rufe wata babbar kasuwar hatsia da dabbobi

Kimanin makonni goma sha hudu kenan tun bayan da rundunar Sojan kasa ta rufe wata babbar kasuwar hatsi da dabbobi dake garin Gaidam ta jahar Yobe, inda tace hakan ya zama wajibi don tabbatar murkushe ayyukan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Sai dai yan kasuwa da abokan cinikkayyarsu sun koka, duba da tsawon lokacin da aka kwashe kasuwar tana rufe, wanda hakan yasa jama’a da dama sun shiga mawuyacin hali, sakamakon kasuwar ta kwashe fiye da shekaru 100 tana aiki.

KU KARANTA: Kungiyar Izala ta ja kunnen zababbun gwamnoni akan neman matan banza

Yan kasuwa suna ji a jikinsu bayan Sojoji sun rufe wata babbar kasuwar hatsia da dabbobi

Yan kasuwa sun koka bayan Sojoji sun rufe wata babbar kasuwa
Source: UGC

Yawancin yan kasuwan suna debo amfanin gonarsu ne kai tsaye zuwa kasuwar, yayin da wasu kuma ke jigilar dabbobinsu daga kauyukansu zuwa kasuwar a duk ranar cin kasuwa don sayar ma abokan cinikinsu kai tsaye.

Wani manomin albasa, Mala Masa Gaidam ya bayyana cewa rufe kasuwar ya zamto tamkar masifa ga manoman kayan lambu, kamarsu albasa, tumatir, tarugu, kankana da ire irensu, inda yace an rufe kasuwar a daidai lokacin da suke girbe amfanin gonarsu.

Ya kara da cewa yawancin kwastomominsu daga jahohin kudancin Najeriya suke zuwa, da kuma kasashen Nijar da kamaru da Chadi, amma a dalilin rufe kasuwar duk sun dauke kafa, don haka suna ji suna gani amfanin gonarsu suka lalace bayan kwanaki 99 suna ajiye.

Haka dai yan kasuwa daban daban da majiyar Legit.ng ta tattauna dasu suka yi ta bayanin irin asarar da suka tafka a dalilin kulle wannan kasuwa, da yadda matakin ya shafi kudaden dake shiga ma gwamnati, rayuwar matasa da kuma rashin aikin yi.

Amma wani babban jami’in tsaro daya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ya zama dole su garkame kasuwar sakamakon yan ta’adda suna amfani da kasuwar wajen kutsa kai cikin jama’a don kai hare hare, tare da sayan kayan abinci, da kuma samun bayanai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel