Wata zukekiyar budurwa ta shiga neman masyi a dandalin sada zumunta

Wata zukekiyar budurwa ta shiga neman masyi a dandalin sada zumunta

Zuwan dandalin sada zumunta na yanar gizo ta zo da abubuwa da dama. Ta taimaki wasu wajen gina kasuwancin su, wasu wajen zama fitattu, wasu kuma wajen kulla alakar soyayyar da ta kai su da yin aure.

Watakila irin wannnan tunanin ne a ran wata zukekiyar budurwa a nan Najeriya da fitar da sanarwar neman saurayi a shafinta na tuwita. salon da matashiyar tayi amfani da shi ya jawo cacar baki a tsakanin jama'a.

A sanarwar da Kennymiles, matashiya mai shekaru 22 ta fitar a shafitan na ta, ta ce ta gaji da irin soyayyar nan ta nesa, a saboda haka ta na son saurayi da ke zaune a gari daya da ita.

Ta rubuta cewar: "ina bukatar saurayi mazaunin garin Abuja, mai tsawon 5'9 zuwa sama. Ina son kowacce kala amma banda baki kirin, sabdoda bana son ya ke bani tsoro da daddare. Ma'aikacin gwamnati ko dan kasuwa. Kar ya kasance mai kiba da yawa, don nima ina da kiba, kuma ya kasance ya iya turanci mai kyau."

Wata zukekiyar budurwa ta shiga neman masyi a dandalin sada zumunta

Wata zukekiyar budurwa ta shiga neman masyi a dandalin sada zumunta
Source: Twitter

Sannan ta cigaba da zayyana abubuwan abubuwan da take bukata a namiji kamar haka: "ya kasance ma'abocin iya saka sutura da daukan wanka. Wanda kuma ya iya girki. Ma'abocin iya zance, saboda ina da yawan surutu. Ba matsolo ba. Mai basira da hikima. Ma'abocin nishadi, amma ba mai zukar hayaki ba.

DUBA WANNAN: Sabon karin albashi ya fara aiki ne daga yau - Fadar shugaban kasa

"Mazaunin Abuja nake so. Zan cika shekaru 22 a watan Agusta, a saboda haka ina son mai shekaru 24 zuwa sama don da yawam masu irin shekaruna basu da cikakken hankali. Na manta na fadi cewar dole ya kasance mai kyan fuska, kabilar da ya fito na da matukar muhimmamci a wurina saboda sanin halin dangi na. Ba aure za mu yi ba, amma dole a kullum mu yi magana."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel