Kalli kyawawan hotunan Aisha Yesufu da mijinta yayin da suke murnar shekaru 21 da aure

Kalli kyawawan hotunan Aisha Yesufu da mijinta yayin da suke murnar shekaru 21 da aure

A jiya ne fitacciyar yar gwagwarmayar nan Aisha Yesufu ta wasu kyawawan hotunanta tare da mijinta inda suke murnar cika shekaru ashirin daya cikakku suna tare a matsayin mata da miji.

Legit.ng ta ruwaito Aisha ta daura wadannan hotuna ne a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda tace a shekaru 21 da suka kwashe tare sun shaku da juna sosai, amma kuma suna sarara ma juna tare da baiwa juna damar cudanya da abokanansa.

Kalli kyawawan hotunan Aisha Yesufu da mijinta yayin da suke murnar shekaru 21 da aure

Kalli kyawawan hotunan Aisha Yesufu da mijinta yayin da suke murnar shekaru 21 da aure
Source: Twitter

KU KARANTA: Tsuguni bai kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutum 10 a Kaduna

Ta kara da cewa dukkaninsu sun taimaka ma juna ta hanyoyi daban daban akan aikin kowannensu domin cima burace buracen da suka sanya a gaba, kuma da taimakon Allah sun samu nasara dukkansu.

Sai dai tace duk da wannan kaunar juna dake tsakaninsu, amma hakan bai hana su samu matsala ba, saboda masu iya magana na cewa zo mu zauna zo mu saba, don haka su kan samu matsala, amma kuma suna warwareta da kansu ba tare da na ji kansu ba.

Kalli kyawawan hotunan Aisha Yesufu da mijinta yayin da suke murnar shekaru 21 da aure

Kalli kyawawan hotunan Aisha Yesufu da mijinta yayin da suke murnar shekaru 21 da aure
Source: UGC

Daga karshe tayi fatan Allah ya kara ma soyayyarsu karko yayin da suka cigaba da zama a matsayin Mata da miji masu kaunar juna har zuwa lokacin da rai zai yi halinsa.

Aisha ta bayyana cewa a ranar 13 ga watan Disambar 1996 ta fara haduwa da Mijinta,amma basu fara soyayya ba sai a watan Agustan shekarar 1997, inda suka yi aure a watan Afrilun shekarar 1998.

Ita dai Aisha Yesufu yar asalin kabilar Edo ce, amma a jahar Kano aka haifeta, kuma a jahar Kano ta girma, tayi karatu a jami’o’I guda uku da suka hada da jami’ar Usmanu Danfodiyo, jami’ar Ahmad Bello da kuma jami’ar Bayero, inda ta kammala karatunta, ta karanci Microbiology.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel