A karon farko tun kafuwar Najeriya, an samu 'sa hannun' mace a kan takardar Naira

A karon farko tun kafuwar Najeriya, an samu 'sa hannun' mace a kan takardar Naira

- An samu sa hannun mace a kan takaradar Naira, a karo na farko bayan kafuwar Najeriya, shekaru 59 da suka wuce

- Priscilla Ekwere Eleje, ita ce mace ta farko da ta taba 'sa hannu' a kan takardar Naira

- Ladi Kwali, ita ce mace ta farko da aka taba saka hotonta a jikin takardar Naira 20 (N20)

A karo na farko a tarihin Najeriya na shekaru 59 da wanzu wa, an samu 'sa hannun' mace, Priscilla Ekwere Eleje, a kan takardar Naira.

Hakan ya biyo bayan tabbatar da Eleje, mukaddashiyyar babban darektan kudi da gudanar wa a babban bankin kasa (CBN), a matsayin darekta.

Eleje, ita ce mace ta farko a tarinhin CBN, da ta taba rike mukamin, sannan mace ta farko da taba 'sa hannu' a kan takardar Naira.

A karon farko tun kafuwar Najeriya, an samu 'sa hannun' mace a kan takardar Naira
Takardar Naira
Asali: UGC

Ladi Kwali, wata mata da ta kware wajen kera tukwanen tabo, ita ce mace ta farko da aka taba saka hotonta a jikin takardar Naira 20 (N20).

DUBA WANNAN: EFCC: Kotu ta yanke wa wasu 'yan N-power biyu hukuncin daurin shekara guda

'Yan cikin gida a CBN, sun shaida wa majiyar Legit.ng cewar gwamnan CBN, Godwin Emefieke, ya na kokari matuka wajen tabbatar da cewar mata sun samu wakilci a cikin babban bankin, musamman a manyan mukamai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel