An kama 'yan sanda 5 a Legas bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 20 da wani mutum

An kama 'yan sanda 5 a Legas bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 20 da wani mutum

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Legas ta kama wasu jami'an 'yan sanda biyar bisa zarginsu da harbe wata budurwa mai shekaru 20, Ada Ifeanyi, a Ajegunle ranar Asabar.

Kakakin rundunar 'yan sanada ta jihar Legas, DSP Bala Elkana, ne ya sanar da hakan a cikin jawabin da ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a kan titin Amusa da ke unguwar Ajegunle.

'Yan sandan sun kara harbe wani mutum, Emmanuel Akomafuwa, mai shekaru 32, a kan titin Babatunde da ke unguwar Olodi Apapa.

"An garzaya da mutanen biyu zuwa asibiti domin ceto rayuwar su, sai dai, an tabbatar da mutuwar Akomafuwa yayin da Emmanuel Akomafuwa yake cigaba da karbar magani bayan an kwantar da shi sakamakon harbinsa da bindiga.

"Jami'an 'yan sanda na ofishin 'Trinity' ne suka yi harbin kuma yanzu haka suna fuskantar matakan ladabatar wa na cikin gida a hedikwatar 'yan sanda ta Legas da ke Ikeja.

An kama 'yan sanda 5 a Legas bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 20 da wani mutum
'yan sanda 5 a Legas da ake zargi da harbe matashiya
Asali: UGC

"An kwace bindigoginsu domin gudanar da binciken kimiyya na musamman. Za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumarsu da aikata laifin kisa, da zarar an kammala bincike kuma an same su da laifi.

DUBA WANNAN: An bawa hammata iska tsakanin Abdullahi Abbas da Kwankwaso

"Jami'an 'yan sandan da aka kama su ne; Insfekta Adamu Usman, Saja Adeyeye Adeoye, Kashim Tijani, Lucky Akigbe da Paul Adeoye, yayin da ake neman daya daga cikin 'yan sandan Insfekta Dania Ojo, ruwa a jallo, bayan ya gudu kafin a kama shi.

"Rundunar 'yan sandan Legas tayi alla-wadai da wannan kisa na farar hula da batagarin 'yan sanda da ke bata sunan 'yan sanda suka aikata.

"Rundunar 'yan sanda ba zata taba nuna gajiwa ba wajen kokarin fitar da balagurbin jami'ai ba daga cikinta. Duk wanda aka samu da laifin aikata kisa ba tare da wata hujja da ta dace da dokar aiki ko ta kasa ba, za ladabatar da su sannan a gurfanar da su," a cewar kakakin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel