Isra’ila ta mayar da masallaci mai cike da tarihi zuwa mashaya da wajen taro

Isra’ila ta mayar da masallaci mai cike da tarihi zuwa mashaya da wajen taro

- Birnin Isra’ila ta mayar da Masallacin Al-Ahmar a Safed zuwa mashaya da dakin bukukuwa

- Biyo bayan mamayar Isra’ila a 1948, a baya an mayar da masallacin zuwa makaranta, cibiyar kamfen din zabe, wajen ajiye kayayyaki da kuma gidan rawan dare

- Sakataren Safed, Khair Tabari, na kira ga taimako don ceto masallacin daga bata

- Tabari yayi korafi kan cewa a yanzu ana bude masallacin don amfanin komai illa ba a bude shi ga musulmai don salloli

Birnin Isra’ila ta mayar da Masallacin Al-Ahmar a Safed zuwa mashaya da dakin bukukuwa.

A cewar Al-Quds Al-Arabi, an fara mayar da masallacin, daya daga cikin masallaci mafi tarihi a birnin Larabawa, zuwa makarantar Yahudawa bayan mamayar Isra’ilawa a 1948.

Legit.ng ta tattaro cewa bayan mayar da masallacin zuwa makarantar Yahudawa, an ci gaba da mayar da ginin zuwa cibiyar kamfen din zaben Likud sannan kuma aka mayar da shi zuwa wajen ajiyear kayayyaki kafin a mayar dashi zuwa wajen rawar dare.

Wani kamfani da ke da nasaba da birnin Isra’ila ta mayar dashi zuwa mashaya da kuma dakin taro sannan an mayar da sunansa zuwa Khan Al-Ahmar.

Isra’ila ta mayar da masallaci mai cike da tarihi zuwa mashaya da wajen taro

Isra’ila ta mayar da masallaci mai cike da tarihi zuwa mashaya da wajen taro
Source: UGC

Sakataren Safed, Khair Tabari, yace yana jiran kotun Nazareth ta yanke hukunci akan korafin da ke neman a bar masallacin sannan a mayar dashi zuwa ga albarkatunta.

KU KARANTA KUMA: Kabiru Marafa ya yi ma Saraki tayin kyakkyawar budurwa sakamakon tallafa ma Zamfara

Yace an tattara duk wasu takardu da ke tabbatar da cewar al’umman Musulmi ce ta mallaki masallacin sannan ta yi kira ga hadin kai daga kungiyoyin siyasa da shahararrun kungiyoyi daban-daban don ceto masallaccin daga rikici.

Kafin a tursasa su barin gidajensu a 1948, Safed ya kasance gidan Palasdinawa 12,000.

Tabari yayi korafi kan cwa a yanzu ana bude masallacin don amfani komai sai dai kawai ba a bude shi ga Musulmai don yin sallah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel