Atiku na cikin tsaka mai wuya

Atiku na cikin tsaka mai wuya

- Jam'iyyar PDP ta na zargin gwamnatin tarayya da jam'iyyar APC da hadawa dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar gadar zare domin ya janye kara daga kotu

- Jam'iyyar ta ce duk wani yunkuri da gwamnatin tarayyar za ta yi ba zai sa Atiku janye karar da ya kai kotu ba

A jiya Alhamis ne 11 ga watan Afrilu kwamitin gudanarwa ta jam'iyyar PDP, ta bayyana cewa babu wani shiri da jam'iyyar APC, ko gwamnatin tarayya za ta yi wanda zai sa dan takakarar ta Alhaji Atiku Abubakar ya janye karar da ya shigar kotu akan zabe.

"Kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Atiku Abubakar ya yi sa'a da har yanzu ba a kama shi ba," kwamitin ta kara da cewa irin wannan kalamai basu kamata ba, ""saboda haka muna kira ga jam'iyyar APC ta san cewar babu wani abu da zai hana Atiku Abubakar kwato hakkinsa a kotu."

Atiku na cikin tsaka mai wuya
Atiku na cikin tsaka mai wuya
Asali: UGC

A wata sanarwa da kakakin kwamitin Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Alhamis dinnan, jam'iyyar PDP ta ce ta na sane da irin makircin da gwamnatin tarayya ta ke hadawa dan takarar shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya hada da jita-jitar da gwamnatin tarayyar ta hada na cewa Atiku ya je kasar Amurka ya aro sojojin haya da za su taya shi kwace zabe a hannun shugaba Buhari, wanda wannan zance bashi da tushe balle makama, kuma sun yi haka ne domin su tayar da hankalin al'umma, sannan kuma su hana Atiku cigaba da gabatar da karar shia kotu.

KU KARANTA: Lai Muhammed ya caccaki Atiku Abubakar

Sanarwar ta kara da cewar, "dama gwamnatin tarayya ta gama kulle kullenta akan irin wannan zargin da suke yi wa Atiku Abubakar, wanda zai kawo tashin tashina a cikin al'umma, sannan su batawa Atiku suna, bayan haka kuma su tilasta shi ya janye karar da ya shigar kotu domin abi mishi hakkinsa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel