Karan kwana: Matashi ya nutse a garin wankan tafki a jahar Kano

Karan kwana: Matashi ya nutse a garin wankan tafki a jahar Kano

Masu iya magana na cewa idan ajali yayi kira, lallai sai an je, ko da kuwa babu ciwo, a irin haka ne ajali yayi kira ga wani matashi dan shekara 22 daya mutu a wani tafki dake cikin unguwar Farawa Ramin Fara, a karamar hukumar Tarauni na jahar Kano.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin hukumar kwana kwana ta jahar Kano, Malam Saidu Mohammed ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Kano.

KU KARANTA: Hansti leka gidan kowa: Kungiyar Izala ta shilla kasar Amurka don aikin Da’awah

Malam Saidu ya bayyana cewa wannan lamari mai ban ta’ajibi ya faru ne da tsakar ranar Laraba yayin da matashin ya shiga cikin tafkin don yin wanka sakamakon tsananin zafin yanayi da ake fama dashi a Kano.

“Da misalin karfe 2:12 na rana muka samu kira daga wani mutumi mai suna Muhammad Bukari, wanda ya bayyana cewa ya hangi gawar matashin mai suna Musa tana yawo a saman ruwan, ba tare da bata loakci ba muka garzaya tafkin, inda muka isa da misalin karfe 2:23.

“Koda jami’anmu suka isa tafkin sun tarar da matashin ya riga ya mutu, amma sun ciro gawar tasa, inda suka mikata ga dagacin unguwar Tsamiyar Mariri, Alhaji Garba Saidu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wani mummunan hadari ya auku da misalin karfe 10:24 na safiyar ranar Laraba akan hanyar Gwarzo zuwa Janguza a karamar hukumar Ungogo ta jahar Kano, kamar yadda kaakakin hukumar ya tabbatar.

Kaakakin yace hadarin ya hada da wata motar Golf ne da babur jin Jincheng da suka yi taho mu gama sakamakon matsanancin gudu da duka ababen hawan biyu suke yi, wanda hakan yayi sanadiyyar jikkatar mutane biyar, yayin da mutane biyu kuma suka suma.

Daga karshe kaakaki Mohammed yayi kira ga masu ababen hawa da su guji yin gudu mara amfani akan titunan don kare kansu, da dukiyoyinsu daga fada ma haddura.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel