Ya auri sa’ar Mahaifiyarsa domin ya samu zuwa kasar Amurka

Ya auri sa’ar Mahaifiyarsa domin ya samu zuwa kasar Amurka

Wani Saurayi mutumin Najeriya ya auri Dattijuwa mai shekaru 61 da haihuwa a Duniya kamar yadda LEGIT.ng ta samu labari. Wannan aure yana cigaba da jan magana yanzu a kafafen sadarwa.

Jude Obi mai shekara 29 shi ne ya auri wata mutumiyar kasar Amurka da ta girme sa nesa ba kusa ba. Wannan mutumi asalin sa ‘Dan wani Gari ne mai suna Orerokpe a jihar Delta da ke Kudu maso Kudancin kasar nan.

Rahotanni sun nuna cewa Dattawan wannan Gari na Orerokpe, sam ba su ji dadin wannan aure ba, duba da yadda Yaron na su da bai kai shekara 30 ba, ya je ya jajibo wanda ta nunka shekarun sa har sau biyu da haihuwa.

KU KARANTA: Forbes tace Michael Jordan ya ba Dala Biliyan 1.7 baya

Ya auri sa’ar Mahaifiyarsa domin ya samu zuwa kasar Amurka

Jude Obi da Amaryar sa 'Yar Najeriya da ya samu a Amurka
Source: Facebook

Kamar yadda labari ya zo mana, Obi yayi wannan aure ne domin ya samu damar shiga Amurka. Obi wanda yake bin darikar Jehovah’s Witness, yayi watsi da surutan mutane, ya auri wannan sahiba ta sa da ta girme sa.

Wani Bawan Allah da ya san yadda aka fara wannan soyayya yake cewa Obi ya hadu ne da Matar ta sa a shafin sada zumunta na zamani na Facebook. Asalin wannan Mata ‘Yar Najeriya amma a yanzu ta ke zama a Amurka.

An samu wani Dattijo a cocin da su ke bauta na masu akidar Kirista na Jehovah da su ka tsaya wajen ganin an daura wannan aure. Wannan mata ta samu wani Mutumi ne da ya tsaya mata a matsayin Waliyyi a kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel