Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Miji ya yi ma matarsa yankan rago a Kano, ya binne gawar

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Miji ya yi ma matarsa yankan rago a Kano, ya binne gawar

Rundunar Yansandan jahar Kano ta sanar da kama wani Magidanci dan shekara 26, Aminu Inuwa dake zaune a unguwar Jakadan Quarters cikin garin Kano da laifin kisan matarsa, Safara’a Aminu mai shekaru 17 ta hanyar yankan rago.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar kama Aminu, inda yace bayan ya kashe matar tasa, sa’annan ya binneta a tsakar gidansu.

KU KARANTA: Babban dalilin da yasa talauci yayi ma Arewa katutu – daga bakin Dangote

DSP Kiyawa ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, kuma hakan ya biyo bayan wata yar sabani data shiga tsakanin ma’auratan, wanda yayi sanadiyyar kaurewar rikici a tsakaninsu.

“Da misalin karfe 11 na safiyar Laraba ne muka samu rahoton cewa a ranar Talata da misalin karfe 12 na rana wani magidanci mai suna Aminu Inuwa ya kashe matarsa Safara’u Aminu a gidansu, sa’annan ya binneta a tsakar gidan.” Inji shi.

Samun wannan mummunan rahoto keda wuya Yansanda suka dira gidan inda suka kama wanda ake tuhuman, haka nan Yansanda sun hako gawar mamaciyar, inda suka mikashi zuwa Asibitin Murtala don binciken gawar, yayin da suke cigaba da rike da Aminu.

Daga karshe kaakakin yace tuni Aminu ya amsa laifinsa, kuma zasu gurfanar dashi gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike akansa. Oh Allah Ya rabamu da mugun ji da mugun gani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel