Yadda mijina ya gamu da ajalinshi a garin yi wa ma'aurata sulhu

Yadda mijina ya gamu da ajalinshi a garin yi wa ma'aurata sulhu

- A garin zuwa ya yi wa wasu ma'aurata sulhu, ya gamu da ajalinshi

- Wasu samari ne suka shigo har cikin gidan da yaje sulhun suka kasheshi

- Matar marigayin ta bukaci hukuma ta hukunta wadanda suke da hannu a kisan mijin nata

Matar marigayi Bonaventure Mkpume, wanda aka kashe a lokacin da ya ke kokarin raba fada tsakanin wasu ma'aurata, ta bayyana yadda mijin nata ya gamu da ajalinshi a gidan ma'auratan.

Chinenye Mkpume, wacce ta ke zaune a kauyen Umueze da ke karamar hukumar Awka, cikin jihar Anambra, ta ce mutuwar mijin nata ya saka iyalansa cikin kunci da tashin hankali, saboda haka ta na bukatar hukuma ta yi adalci wurin yankewa wadanda su ka aikata kisan hukunci.

"Muna zaune a gida ni da mijina, sai wata makwabciyar mu ta kirani a waya ta ke fada mini cewar mijinta ya na dukanta.

Yadda mijina ya gamu da ajalinshi a garin yi wa ma'aurata sulhu
Yadda mijina ya gamu da ajalinshi a garin yi wa ma'aurata sulhu
Source: Depositphotos

"Na yi niyyar na je ni daya na raba fadan, amma mijina ya takura akan shi ma sai yaje, bai san da cewar ajali ne ya ke kiranshi ba," in ji matar.

"A lokacin da muke yiwa ma'auratan nasiha sai ga wasu samari su biyar, sun shigo gidan da adduna a hannunsu.

"Su na zuwa suka hau mijina da sara, wanda shine ya ke tsaye a gaban kofar gidan, a take suka yanke mishi hannu, sannan suka sareshi a wuya da adda."

KU KARANTA: 'Tun ina 'yar shekara 8 mahaifina ke kwanciya da ni'

Mrs. Mkpume ta ce a lokacin da samarin suka shigo gidan, matar da ta kira su sai ta janye mijinta suka gudu daki su ka kulle, suka barsu ita da mijinta a gurin.

Mahaifiyar marigayin, Mrs Grace Mkpume, wacce ta fashe da kuka, ta bukaci a hukunta wadanda suke da hannu wurin kashe dan nata guda daya tilo.

Bayan haka kuma, mai magana da yawun hukumar 'yan sanda na jihar Haruna Mohammed, ya ce har yanzu DPO na yankin bai basu rahoton halin da ake ciki ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel