Zaben Kaduna: Isa Ashiru yana kalubalantar nasarar APC a Kotu

Zaben Kaduna: Isa Ashiru yana kalubalantar nasarar APC a Kotu

Mun samu labari cewa ‘Dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kaduna a zaben da aka yi kwanan nan watau Muhammad Isa Ashiru Kudan yace yana na a kan bakan sa na karbo nasara a kotun zabe.

Rt. Hon. Isa Ashiru Kudan bai yi na’am da sakamakon zaben gwamna da aka yi a jihar Kaduna ba don haka ya garzaya kotu. Kudan ya tabbatarwa Magoya bayan sa cewa yanzu haka su na kotu, kuma za su samu nasara a kan APC.

Honarabul Ashiru Kudan wanda yake ganin shi ne ya lashe zaben da aka yi a farkon Watan Maris a Kaduna ba gwamna Malam Nasir El-Rufai na jam’yyar APC ba, ya jinjinawa Mabiyan sa da irin goyon bayan da su ke badawa.

KU KARANTA: Babban Sanatan Arewa ya caccaki shirin APC na kakaba Shugaban Majalisa

Zaben Kaduna: Isa Ashiru yana kalubalantar nasarar APC a Kotu
Ashiru Kudan yace shi ya ci zaben Kaduna ba Gwamna El-Rufai ba
Asali: Twitter

Yanzu haka dai ‘dan takarar gwamnan yace magana ta fara nisa a gaban kotun sauraron korafin zabe inda yake sa ran karbe nasarar da ya samu a zaben Watan jiya. Kudan yayi wannan jawabi ne a shafin Tuwita a karshen makon jiya.

‘Dan takarar na PDP ya bayyana cewa ba zai amince da sakamakon zaben da aka yi a jihar Kaduna ba tun kwanaki baya, ‘dan takarar jam’iyyar hamayyar yana ikirarin cewa shi ne yayi nasara amma APC mai mulki ta murde zaben.

A jiya kuma dai kun ji cewa ‘Dan takarar PDP a Kano, Abba K. Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya bayyana cewa Lauyoyin sa sun tattara hotuna hujjojin da za a bukata a gaban kotun karar zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel