'Yan sanda sun aika da wani shugaban direbobi lahira

'Yan sanda sun aika da wani shugaban direbobi lahira

- Wata mata ta kawo karar wasu 'yan sandan Najeriya da suka aika da mijinta lahira, da duka da bayan bindiga

- Matar marigayin ta bukaci gwamnti ta yi adalci wurin hukunta wadanda su ka aikata laifin kisan

- Ta bayyana cewa bayan sun harbe shi bindigar ba ta shiga, sai suka yi amfani da bayan bindiga suka dinga dukanshi har sai da ya daina motsi

Matar shugaban kungiyar direbobi ta kasa reshen jihar Uyo, Mrs Margaret Udofia, ta bayyana yanda jami'an 'yan sanda su ka kashe mata mijinta Mr Ubong Udofia, a tashar mota.

Ta bayyanawa manema labarai cewa mijinta ya mutu a hannun 'yan sanda. Margaret ta ta ce mijinnata da ma shine wanda ya ke daukar nauyinsu, yanzu kuma ya mutu ya bar ta da yara guda tara.

'Yan sanda sun aika da wani shugaban direbobi lahira
'Yan sanda sun aika da wani shugaban direbobi lahira
Asali: Twitter

Ta yi kira ga shugaban 'yan sanda na kasa, da kwamishinan 'yan sandan jihar, da kuma gwamnan jihar Udom Emmanuel da su tabbatar da abin hakkin mijinta da aka kashe.

"Ina rokon shugaban hukumar 'yan sanda da kada yayi watsi da rokon da na ke mi shi, saboda shaidu sun nuna cewa an kashe mijina ne da gangan, saboda mijina da sauran 'yan banga ba su daki jami'in dan sandan da ake zargin su da sun daka ba. "

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga wani taron gaggawa da 'yan kungiyar CAN

A cewarta, wani jami'in dan sanda ya tsaya da motarsa ya na daukar fasinja a kusa da tashar motar Itam, sai 'yan bangar da su ke aiki da mijina su ka ganshi su ka yi mishi magana, a ta ke a wurin rikici ya kaure a tsakanin su.

"Mijina ya na zaune a cikin wata motar ya na jiran mai motar, bai san da cewar wancan dan sandan ya kira, 'yan uwanshi ba, bai aune ba sai ji ya yi sun bude mishi wuta."

A cewarta, 'yan sanda da su ka budewa mijin nata wuta su ka ga cewar bindigar ba ta cin shi, sai suka koma amfani da jikin bindigar su na dukan shi, har sai da su ka tabbatar da ba ya motsi.

DPO na ofishin 'yan sanda da ke Itam, CSP Francis Irabor, wanda ya ziyarci mamacin a asibiti. Ya yi alkawarin yin binciken da ya kamata akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel