Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Fintiri a Adamawa

Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Fintiri a Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta gabatar da takardar shadar cin zabe ga dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri.

A ranar Alhamis, 28 ga watan Maris ne dai aka kammala zaben gwamnan na jihar Adamawa, inda dan takarar jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ya kayar da gwamna mai ci, Mohammed Bindow na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jam'iyyar PDP ta samu nasarar ne da kuri'u dubu 376,552, yayin da jam'iyyar APC mai mulkin jihar a yanzu ta zo na biyu da kuri'u 336,386.

Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Fintiri a Adamawa
Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Fintiri a Adamawa
Asali: UGC

Kwamishinan Zaben jihar, Farfesa Andrew Haruna, ne ya kaddamar da Amadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar.

KU KARANTA KUMA: An kama wasu Fastoci 2 bisa zargin kashe mijin yayarsu

A wani lamar na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa na shirin dakatad da gurfanar da Sanata Bala Mohammad bayan ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya.

A dokar kasa, duk wanda aka zaba gwamna ko shugaban kasa yana samun kariya daga kowani irin bincike har sai ya sauka daga mulki.

Bala Mohammed, wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi karkashin Peoples Democratic Party PDP), da aka gudanar ranar 9 ga watan Maris, ya lallasa gwamna mai ci, Mohammaed Abubakar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel