Zaben Adamawa: PDP ta lashe mazabu 5, APC ta samu 1 a Michika, karamar hukumar Mubi ta arewa

Zaben Adamawa: PDP ta lashe mazabu 5, APC ta samu 1 a Michika, karamar hukumar Mubi ta arewa

Jam’ iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta lashe mazabu biyar a Minchika da karamar hukumar Mubi ta arewa da ke jihar Adamawa, yayinda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kamala zaben gwamna da aka sake a jihar a yau, Alhamis, 28 ga watan Maris.

Hakazalika, jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe rumfa daya, mazabar Moda Dlaka a karamar hukumar Michika yayinda ta samu kuri’ u 116 inda PDP ta samu kuri’u 101.

Zaben Adamawa: PDP ta lashe mazabu 5, APC ta samu 1 a Michika, karamar hukumar Mubi ta arewa
Zaben Adamawa: PDP ta lashe mazabu 5, APC ta samu 1 a Michika, karamar hukumar Mubi ta arewa
Asali: UGC

Ga sakamakon karshe na zabe daga mazabu shida cikin 44 da abun ya shafa a wurare 28 da aka yi rijista a jihar a kasa:

Michika LGA

Fwa unit

PDP – 161

APC – 3

Jigalambu unit

PDP – 248

APC – 7

Moda Dlaka unit

PDP – 101

APC – 166

Mubi North LGA

Fagui Unit

PDP – 204

APC – 1

Mitiri Unit

PDP – 266

APC – 2

Ribawa Unit

PDP – 261

APC – 7

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel