'Yan bindiga sunyi awon gaba da 'dan sanda da wasu mutane a Edo

'Yan bindiga sunyi awon gaba da 'dan sanda da wasu mutane a Edo

'Yan bindiga sun sace wani dan sanda mai suna DSP Godwin da wasu mutane hudu a Ubiaja, headkwatan karamar hukumar Esan ta Kudu a jihar Edo.

DSP Godwin yana kan hanyarsa ne na zuwa Asaba yayin da 'yan bindigan suka tsayar da motar da ya ke ciki domin sace mutanen da ke motar.

Majiya daga rundunar 'yan sanda ta ce an tisa keyar DSP Godwin da wasu mutane daga cikin motar zuwa daji.

DUBA WANNAN: Yadda kananan yara masu talla ke yada cutar Kanjamau a Borno

'Yan bindiga sunyi awon gaba da 'yan sanda da wasu mutane a Edo
'Yan bindiga sunyi awon gaba da 'yan sanda da wasu mutane a Edo
Asali: Twitter

Majiyar har ila yau ta ce 'yan bindigan sun harbe wani fasto da bayan sun tsayar da motarsa kuma a halin yanzu yana asibiti yana jinya.

An gano cewar 'yan sandan sun baza jami'ansu na musamman a dajin da ke kusa da Ewatto, Ubiaja da Okhuessan da niyyar ceto abokin aikinsu da sauran mutanen.

Kakakin rundunar 'yan sanda, DSP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa suna kyautata zaton samun labari mai dadi idan jami'ansu sun fito daga dajin.

Ya kara da cewa rundunar 'yan sandan tana iya kokarinta domin waiwayar jami'anta na musamman da ke Ubiaja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel