Hukumar INEC ta bai wa zababben gwamna da yan majalisan jihar Borno takardun shaidan cin zabe

Hukumar INEC ta bai wa zababben gwamna da yan majalisan jihar Borno takardun shaidan cin zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a ranar Laraba, 26 ga watan Maris a Maiduguri, ta gabatar wa zababen gwamnan Borno Babagana Zulum takardan shaidar cin zabe.

Hukumar har ila yau ta gabatar da takardan shaidar cin zabe ga zababbun mambobin majalisar jiha guda 28.

AVM Ahmed Mu’azu (mai ritaya), kwamishin hukumar INEC na tarayya da ke kulawa da Borno, Adamawa da Taraba, wanda ya samu taimakon kwamishinan hukumar zabe, Mohammed Magaji, ne ya gabatar da takardun shaidan ga zababbun masu rikon ofishin siyasan.

Mu’azu yayi kira ga Zulum da sauran zababbun wakilai da su cika alkawura da suka dauka a lokacin yakin neman zabe don ci gaban jihar da kasa baki daya.

Hukumar INEC ta bai wa zababben gwamna da yan majalisan jihar Borno takardun shaidan cin zabe
Hukumar INEC ta bai wa zababben gwamna da yan majalisan jihar Borno takardun shaidan cin zabe
Asali: Twitter

Ya ce: “Ina taya masu zabe wadanda suka zabe ka murna akan zaban ka da suka yi, sun kasance masu biyayya ga doka duk da kalubale da yankin arewa maso gabas ke fuskanta.

"Zuwa ga zababbun yan yakara, ya zamo dole ku tabbatar da cewa kun cika alkawaran da kuka yi a lokacin yakin neman zabe don ci gaban jihar da kasa.”

Mu’azu har ila yau ya yabi jami’an zabe, jami’an tsaro, jam’iyyun siyasa; da masu ruwa da tsaki bisa gudanar da zabbuka cikin kwanciyar hankali da lumana.

Yayin da yake mayar da martani, Zulum, ya sha alwashin kara kaimi akan nasarorin da aka samu a gwamnatin Kashim Shettima.

Ya kara da cewa gwamnatinsa zata kafa shirye shirye don magance asalin ta’addancin kungiyar Boko Haram, zata kuma samar da ayyuka ga mafi yawancin matasa.

Zababben gwamnan nemi goyon bayan zababbun yan majalisan jiha da na kasa, don bashi damar kawo ci gaba a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta rahoto cewa Gwamna Kashim Shettima ya kasance daga cikin wadanda suka halarci taron, tare da mataimakinsa Usman Durkwa, Sanata Ali Ndume da Habu Kyari, tare da mambobin majalissu na kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel