Yanzu Yanzu: Wani ginin ya sake rusowa a Lagas

Yanzu Yanzu: Wani ginin ya sake rusowa a Lagas

Rahotanni sun kawo cewa wani gini ya sake rushewa a unguwar Kakawa da ke birnin Lagas a ranar Litinin, 25 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Wamakko da Ahmed Aliyu sun musanta kiran Gwamna Tambuwal a waya

A cewar wani mazaunin unguwar, babu wanda ya garkame a karkashin ginin, saboda an sanya ma ginin alama cikin wadanda za a rusa kuma mazauna gidan sun dade da barin gidan.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa ani abun bakin ciki ya afku a ranar 13 ga watan Maris, lokacin da wani ginin bene mai hawa uku ya ruguzo wanda a saman akwai makaranatr Firamare, gidaje da shagunan haya a Itafaji, birnin Lagas.

Lamarin yayi sanadiyar rasa rayuka da dama ciki harda na wasu daliban makarantar Firamare.

Mahaifin daya daga cikin daliban da abun ya shafa, Abdulfatah Ayoola, ya kasancee cikin wani hali bayan an tabbatar da mutuwar dansa mai shekaru shida, Fawaz. An tattaro cewa an tono gawar Fawaz daga cikin rusasshen ginin da misalin karfe 2:00 na ranar da abun ya afku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel