Yar kunar bakin wake, mai suna Zara, ta shiga hannu a jahar Borno

Yar kunar bakin wake, mai suna Zara, ta shiga hannu a jahar Borno

Wata karamar yarinya mai shekaru goma sha uku mai suna Zara, wanda mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka tilasta mata kai harin kunar bakin wake ta hanyar daura mata bamabamai a jikinta, ta shiga hannun matasan Sojojin sa kai a jahar Borno.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an kama Zara ne a daidai lokacin da take kokarin shiga cikin barikin Sojoji na Giwa Barracks dake cikin garin Maidugurin jahar Borno, yayin da take dauke da jigidan bama bamai.

KU KARANTA: Zaben Gwamnan Kano: Kwamishina ‘Maza kwaya Mata kwaya’ ya kai ma Malaman Darika ziyara

Sai dai da ta shiga hannu ta fasa kwai, inda tace su yan mata hudu mayakan Boko Haram suka daura ma jigidan bama bamai, sa’annan suka daukosu daga karamar hukumar Banki da nufin su kai harin kunar bakin wake.

Inda suka ajiyeta akan hanyar Giwa Barracks, yayin da suka wuce da sauran mata uku zuwa wasu sassan garin Bama domin su tayar da bom ta hanyar kashe kansu da duk mutanen dake zagaye dasu.

A sakamakon haka ne matasan Civilian JTF suka umarci jama’a da kowa ya koma cikin gida har sai an kamo sauran matan musamman tunda babu wanda yasan inda suka nufa, daga bisani kuma kwararrun Yansanda masu kwace bom suka hallara don kwance bom dake jikin Zara.

A wani labarin kuma, Kungiyar ta’addanci ta mayakan Boko Haram sun kaddamar da wata mummunan hari a kokarinsu na afkawa cikin garin Michika na jahar Adamawa tare da kokarin karbe garin, sai dai sun samu tirjiya daga dakarun rundunar Sojin kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel