Ina da sana'ar da zan dogara da kaina ko da na bar harkar fim - Adam Zango

Ina da sana'ar da zan dogara da kaina ko da na bar harkar fim - Adam Zango

Shahararren jarumin na dandalin shirya fina-finan Hausa kuma mawakin zamani, Adam A Zango ya bayyana cewa yana da sana'ar da zai iya dogaro da kansa ko da bayan ya bar sana'ar shirya fina-finai.

Jarumin ya bayyana hakan ne, a cikin wani zungureren rubutu da ya wallafa a shafukan sa na sada zumunta mai taken "Kannywood din yanzu ba kamar ta baya bace".

Rubutun da ya yi tsokaci sosai akan irin yadda goyon bangarorin siyasa ke kokarin kawo cikasa a hadin kan 'yan wasan Hausa.

Ina da sana'ar da zan dogara da kaina ko da na bar harkar fim - Adam Zango
Ina da sana'ar da zan dogara da kaina ko da na bar harkar fim - Adam Zango
Asali: UGC

Haka ma jarumin ya bada misalin yadda rashin hadin kai ya janyo rashin tallafawa wasu 'yan wasa da suka tsinci kansu cikin yanayin jarabawar rayuwa.

A shafinsa na Instagram Adam Zango ya nuna alhini kan yadda a yanzu jaruman ke dar-dar wajen koda yin sharhi ne idan ya wallafa wani rubutu ko hoto a shafinsa don gudun kada fuskanci matsala a wajen ubannin gidansu.

Yace tun yanzu ma da yake raye kenan idan aka ce babu ransa wani hali iyalinsa za su tsinci kansu.

KU KARANTA KUMA: Ali Nuhu ya samu mabiya miliyan 1 cif a shafin Instagram

Ya rubuta a shafinsa: “Yau an wayi gari a Kannywood duk wanda yayi posting ko Reposting ko comments ko Liking din hotona toh ya shiga masifa abincinsa ya yanke a masana’anyar. Wai fat un ina da rai fa kenan ballantana ace na bar duniyar. Wani hali yayana zasu shiga? Amma babu kimai akwai Allah.

“Allah ya kara mana tsawon raid a lafiya zamu gamu nan gaba kadan. Idan maye ya manta uwar da bazata manta ba.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel