Dan uwana ya bani kunya, ya gaza wa mutanen Kwara – Yar’uwar Saraki

Dan uwana ya bani kunya, ya gaza wa mutanen Kwara – Yar’uwar Saraki

Yar’uwar Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, Oyinkansola Saraki ta caccaki dan uwanta a wani shirin talbijin, tace ya gaza tunanin jama’a a lokacin da yayi aiki a matsayin gwamnan jihar Kwara.

Oyinkansola ta soki kokarin dan uwanta sannan ta roki mutaneen Kwara yafiya yayinda ta bayyana a shirin TVC a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris.

Shugaban majalisar dattawa ya kasance zababben gwamnan Kwara a 2003. Bayan kammala mulkinsa, yaki bin umurnin mahaifinsa na tallafa yar’uwarsa, Gbemisola tsouwar Sanata domin ta gaje shi.

Maimakon haka sai ya marawa gwamna mai mulki, Ahmed Abdulfatai baya inda ya kayar da yar’uwar tasa.

Dan uwana ya bani kunya, ya gaza wa mutanen Kwara – Yar’uwar Saraki
Dan uwana ya bani kunya, ya gaza wa mutanen Kwara – Yar’uwar Saraki
Asali: Depositphotos

Shugaban majalisar dattawan ya samu cikasa a lamarin siyasarsa a zaben 2019. Bayan gaza samun nasarar komawa majalisar, wanda dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ibrahim Oloriegbe ya doke shi, dan takarar gwamnan da ya daura Razak Atunwa ma ya sha kaye a hannun dan takarar APC, Abdurahman Abdurazaq, wanda hakan ya dukufar da mambarin siyasar Saraki baki daya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta ziyarci wadanda ginin Lagas ya rufto masu a asibiti

Da take martini kan lamarin, Oyinkansola tace dan uwan nata ya bata kunya matuka kan yadda ya jagoranci jihar.

Ta roki zababben gwamnan jihar da ya bata dammar da za ta gyara kuskuren da iyalan suka yi domin gudun bacin suna.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel